Duk da tata-burza da take tsakanin Dan wasa Mesut Ozil da Mikel Arteta, sai gashi dan wasa Ozil ya fayyace cewa, baya nadamar kulla yarjejeniya da kungiyarsa, Arsenal da kawo yanzu ya shafe akala shekaru 7 tare da ita.
Ozil ya sauya sheka daga Real Madrid zuwa Arsenal A shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 42 da rabi, inda kuma a tsawon lokacin da suke tare ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofunan FA 3, da na Community Shield 1, haka zalika ya lashe kyautar dan wasa mafi kwazo a kakar wasa ta 2015/2016.
Sai dai daga bisani, tauraron Dan wasan tadaina haskawa, musamman lokacin da Sabon mai horaswa na kungiyar ya zo, Mikel Arteta.
Amma duk da wannan, Ozil yace bai taba yin nadamar kulla yarjejeniya da Arsenal ba.