Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta gayyaci shuwagabanin hukumar da ke kula da malamai ta jihar Bauchi ‘Teachers Service Commission’ don su bayyana a gabanta don yin bada bahasi kan saida takardun ɗaukan aikin koyarwa da ke gudana a halin yanzu a kan kuɗi naira ɗari biyar a maimakon ɗaya ɗaya kacal.
Mamba mai wakiltar mazaɓar Dass Maryam Garba Ɓagel itace ta kawo ƙudirin a gaban majalisar ta ce hukumar da ke kula da malamai na jihar Bauchi ta saida takardar guraben aiki a kan naira dari biyar 500 a maimakon naira 100 kacal da suka sayar a kwanakin baya, inda take cewa “Hukumar ɗaukan malamai ta saida fom wajen guda dubu biyar 5,000 a kan kuɗi har naira 500 wanda kuma fom ɗin nan a naira 100 ake saida shi”.
A bisa haka ne ta buƙaci majalisar ta gayatoci shuwagabanin TSC domin su bada bahasi kan wannan lamarin. Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban hukumar kula da malamai ta jihar Bauchi M.N Fa’izu Saleh inda ya ƙi cewa uffan kan lamarin.
Haka zalika a yayin zaman mamba mai wakiltar Azare/Maɗangala Tijjani Muhammadu Aliyu ya buƙaci gwamnatin jiha da ta gyara asibitin Azare “Da yawan asibitocinmu za ka lura suna cikin wani hali wanda babu kyan gani”.
Ya ce babban asibitin garin na Azare ya riga ya gama lalacewar da har yana hana ma’aikatan yin aikinsu yanda ya kamata, a cewarsa ƙananan hukumomin da suke da makwafta da Azare na zuwa wannan asibitin a don haka da buƙatar a yi masa garan bawul. Da ya ke jawabin goyon baya kan ƙudurin mamba mai wakiltar Katagum Ibrahim Bello ya yi ƙira ga gwamnati da ta sanya dokar ta ɓaci a sashin lafiya da ke jihar domin samun gyarar da ta dace.