A makaon da ya gabata ne, Bankin Zenith Plc, ya fitar da sakamakon takardar binciken kudinsa, na ranar 31 ga watan Disambar 2024.
Sakamakon ya nuna cewa, Bankin ya samo kaso 86 a cikin dari, na ribar da ya samu, wadda ta karu, daga Naira tiriliyan 2.12 a shekarar 2023, zuwa Naira tirliyan 3.97.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
A cewar samakamon takardar binciken kudin ta Bankin ta 2024 da aka gabatar wa da Hukumar Kula da Hada-Hadar Musayar Kudade ta Kasa NGD, ribar da Bankin Zenith Plc ya samu, ta karu zuwa kashi 138 a cikin dari.
Bayanj biyan haraji, ribar da Bankin Zenith ya samu ta karu zuwa kashi 67, inda ta kai daga Naira tiriliyan 1.3 a shekarar 2024, sabannin ribar Naira biliyan 796 da Bankin ya samu a shekarar 2023.
Kudin ruwan da Bankin ya samu ya karau zuwa kashi 135 daga Naira tiriliyan kashi 736, sabanin Naira tiriliyan 1.7 da Bankin ya samu a shekarar 2023.
Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.
Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024.
Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya.
Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1.
Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta kai ta Naira 4.00, wadda ta kai jimlar ribar shiyar Naira 5.00 da ya samu a shekara.
Shugaba kuma Manajin Darakta na rukunonin Bankin Dakta Adaora Umeoji, da yake yin bayani kan wannan nasarra da Bankin ya samu ya sanar da cewa, nasarar da Bankin ya samu a shekarar, ta nuna irin jajircewar da Bankin ya ke ci gaba da yi, wajen gudanar da ayyukansa, musamman ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.
“Zamu kuma ci gaba da mayar da hankali wajen kara habaka fanninin mu na hada-hadar kudade, kara inganta ayyukan mu da farantawa abokan huddar mu da masu ruwa da tsaki rai,”. Inji Bankin Dakta Adaora.
A cewar Shugaban na rukunonin Bankin na Zenith, za mu kuma ci gaba da kara karfafa wanzar da shugabancin mu a fannin hada-hadar kudade na kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp