Ganin cewa ana dab da bankwana da shekarar 2023, LEADERSHIP Hausa ta yi nazarin manyan abubuwa uku da suka fi daukar hankulan ‘Yan Nijeriya a shekarar.
Rashin kwanciyar hankali ta yadda ‘yan kasa za su samu sukunin gudanar da harkokinsu ya yi matukar ci wa jama’a tuwo a kwarya, kana sai batun gudanar da zaben 2023 wanda jam’iyyar APC da take matsayin adawa kafin zaben 2015 ta ci gaba da jan zarenta bayan lashe zaben shugaban kasa da na galibin gwamnonin da aka yi a watan Fabrairu da Maris.
- INEC Ta Tilasta Wa Daraktocinta 4 Yin Ritaya
- Kotu Ta Bai Wa Trump Damar Shiga Zaben Fidda Gwani A Amurka
Abu na uku da kusan za a iya cewa ya sauya akalar mafi aksarin rayuwar ‘yan kasar bisa tsadar kayayyakin masarufi shi ne cire tallafin mai wanda sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da yi a jawabinsa na karbar ragamar mulki.
Har ila yau, mun yi bitar tirka-tirkar canjin wasu takardun naira.