Ranar 29 ga watan Mayun 2023, da aka rantsar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin Shugaban Nijeriya na 16, za ta ci gaba da kasancewa a cikin tarihi bisa yadda sanarwar da sabon shugaban ya yi na cire tallafin mai za ta ci gaba da kai-komo a zukatan ‘Yan Nijeriya musamman wadanda ke matukar jin radadin abin.
Duk da yake Tinubu ya yi bayanin cewa zai cire tallafin tun a lokacin da yake yakin neman zabe, amma kuma abin ya zo da ba-zata. Kasancewar man fetur ya shafi kusan dukkan bangarorin rayuwar al’umma, nan take aka fuskanci tsadar rayuwa tun daga farashin sufuri da hauhawar farashin kayan masarufi, wanda hakan ya jefa al’ummar Nijeriya cikin halin ni-‘yasu.
- Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin ‘Yan Ta’adda A Filato
- Boss Mustapha Ya Karyata Zargin Satar Dala Miliyan 6.3 Daga CBN
Lokacin da Tinubu ya sanar da cire tallafin gaba daya, dokar alkinta albarkatun man fetur ta (PIA) ta riga ta cire tallafin kusan wata 15 da suka gabata amma gwamnatin Shugaba Buhari ta san dabarar da ta shigar da Naira Tiriliyan 3.36 cikin kasafin kudin shekarar 2022 don ta tsawaita lamarin tallafin zuwa watan Yuni na shekarar 2023.
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana rashin jin dadinta da janye tallafin man, inda ta yi korafin cewa ya kamata gwamnati ta fadada tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da fito da tsare-tsaren da za su rage wa al’umma radadin da janye tallafin zai haifar a rayuwar yau da kullum, ta kuma yi barazanar tsuduma yajin aiki in har gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba. Amma tattaunawar da bangaren gwamnati da shugabannin kungiyar suka yi ta haifar da fahimtar juna duk kuwa da wata kotun tarayya ta haramta wa kungiyar kwadagon shiga yajin aikin, kungiyar kwadagon ta janye yajin aikin da ta shirya shiga ranar Laraba 6 ga watan Yuni.
Don fahimtar halin da al’umma suka shiga sakamakon cire tallafin wani mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Malam Bashir Dalhatu ya yi nazari da bibiyar rayuwar ‘yan uwa da abokan arziki, inda ya yi nazari halin da magidanci mai ‘ya’ya biyu ke ciki sakamakon cire tallafin man a Nijeriya.
Ya ba da misali da kudin da magidancin zai iya kashewa a abincin rana daya kamar haka: abincin safe, burodi =N600, kosai =N300, ruwan shayi ba madara= N200, ya kama= N1,100, a wata N1,100 sau 30 = N33,000. In kuma in zai yi wainar fulawa, ga yadda za ta kasance, fulawa= N400, Mai N250, Magi N100, kayan miya N50, koko N200, sukari N150, gawayi N100, ya kama: N1,250, kenan a wata, abin da za a kashe ya kama N1,250 sau 30 = N37,500 a cin abin safe kwai.
Abinci rana kuma an kiyasta zai kashe N29,100 a duk wata a abincin dare kuma zai iya kashe N21,900, in aka hada da kudin ruwan sha na N4500 duk wata zai kashe N88,500 kenan a duk wata idan zai sha shayi ba madara kuma ba zai ci abinci da kifi ko nama ba. Idan kuma wainar fulawa zai yi da safe zai kashe N93,000 a wata shi ma dai ban da kifi da nama.
Wannan lissafin na magidanci ne mai ‘ya’ya biyu kuma ba a saka kudin haya, kudin wuta, rashin lafiya, kudin zuwa aiki, omo, sabulu da sauran su.
Idan aka lura da mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikatan Nijeriya wanda ma har zuwa yanzu wasu jihohi da kananan hukumomi ba su fara aiwatar da biyan albashin ba, tabbas magidanta a Nijeriya sun shiga halin matsi sosai.
Haka kuma ba a hada da kudin makarantar boko na yara, da kudin makarantar islamiyya da na kayan sawa ba wanda dukkan su cire tallafin mai ya shafe su.