Sanarwar da Gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ta sauya wasu takardun kudi tare da fara bayarwa daga ranar 15 ga Dismba, 2022 zuwa 31 ga Janairu, 2023, na daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a 2023 saboda yadda lamarin ya shafi rayuwar ‘Yan Nijeriya.
Duk da shiga maganar da Majalisar Kasa ta yi na neman Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin da ya bayar na daina karbar tsofaffin takardar kudin 1000, 500 da 200, Babban Bakin ya ce ba za a kara koda minti daya ba a wa’adin da aka sanya na ranar 31 ga watan Janairu 2023, inda hakan ya sa ‘yan Nijeriya cikin dimuwa. Amma daga bisani da gwamnati ta ji matsin lamba, sai ta kara wa’adin zuwa 11 ga Fabrairu, 2023.
- Harin Filato: Gwamnati Ba Za Ta Huta Ba Har Sai An Hukunta Maharan – Shettima
- NAF Ta Lalata Haramtattun Wuraren Tace Mai Guda 6 A Ribas
Al’umma sun shiga cikin dimuwa da fargaba. Karancin takardun sabbin kudin da rige-rigen sauyawa a bankuna ya kara haifar da wahalhalu ga ‘yan kasa. Masana sun bayyana cewa, CBN ya samar da sabbin kudin ne na Naira Biliyan 200 kuma abin da ake bukata ya kai fiye da Naira Tiriliyan 3.1 abin da ya sa masana ke ganin shi ne babban dalilin karancin sabbin kudaden.
Masu harkar canjin kudin sun mayar da harkar canjin kasuwanci inda aka rika sayar da sayar da sabbin a unguwar zone 4 da ke babba birnin tayarra Abuja.
Wani karin abin haushi game da canjin kudin shi ne, hanyoyin da ake hada-hadar kudin ta intanet duk sun rika toshewa ta yadda abin ya zama kasada, imma kudin da aka tura ya tafi ko ya salwanta.
Ba a wannan karon aka fara canza fasalin kudi a Nijeriya, shugaba Buhari a lokacin da ya jagorancin Nijeriya a matsayin soja a shekara 1983 ya yi canjin kudi wanda ‘yan Nijeriya da dama suka tafka asara sabosa kasa cimma wa’adin mayar da tsofaffin kudin zuwa banki wannan ya sa wadanda suka san irin dambarwar da aka fuskanta a waccan lokacin suka shigta dimuwa da fargabar halin da za a iya shiga in har wa’adin ya kulle mutum bai kai kudinsa banki ba.
Canjin kudi na wannan karon ya zo ne ana tsakiyar hada-hada da gangamin siyasar 2023, kuma kowa yana sane da cewa, harkar siyasa a kasar nan abu ne da ya yake tafiya da kudi, ma’ana iya kudin ka iya shagalin ka
Dimuwa da tashin hankalin da mutane suka shiga sun sa wasu na ikirarin ba za su zabi jam’iyya mai mulki ba, abin da ya sa dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Biola Ahmed Tinubu ya bara, ya yi korafin cewa, an kikiro da lamarin tun da farko don kawo masa cikas a yunkurinsa na zama shugaban Nijeriya.
Masu lura da al’amurran yau da kullum sun bayyana cewa, jifar tawagar shugaban kasa a yayin da ya kai ziyara garin Katsina don kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da kuma ihun da aka yi a ziyarar kaddamar da wasu ayyukan raya kasa a Jihar Kano, inda wasu yara suka yi jifa da furuce-furucen “Ba ma yi! Bama son canji, da sauransu”, tabbas a bayyane yake cewa, al’amarin canjin ya kara wa gwamnatin Shugaba Buhari bakin jinni.
A wata sabuwa kuma, da yake bayani a wani zauren tattauna wanda wasu shaharrun Lauyoyi da ‘yan Jarida ke gabatarwa a shafin intanet, Manjo Hamza Al-mustapa (Mai Ritaya) ya ce, canjin kudn da aka yi ba komai ba ne illa damfara, yana mai cewa, “419 (Damfara) aka shirya domin a wahalar da ‘yan Nijeriya, idan kuma Emifiele ya isa, ko shi, ko mukarrabansa su fito fili su karyata in ban tona asiri ba” in shi ji.
Haka kuma Gwamnan JIhar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa, akwai wasu a fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da suke neman kayar da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Yanzu haka dai tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele na fuskantar tuhuma daban-daban a kan badakalar kudi a gaban kotu.