Nijeriya ta kwashe tsawon wasu shekaru tana fama da tabarbarewar tsaro wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayukan jama’a da dukiyoyi da dama. Duk da cewa a 2022, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin ba zai gadar wa shugaban kasa na gaba da matsalar tsaro ba, amma hakan bai hana matsalar ta tsaro ci gaba da addabar Nijeriya a 2023 ba, wanda gwamnatocin kasar ke ta fafatukar magancewa.
Tun daga farkon shekarar ta 2023 har zuwa karshenta da muke gani yanzu, akwai mayakan kasar da ke fafatawa da ‘yan ta’adda a karkashin shirye-shirye masu yawa na rundunonin tsaro.
- Tinubu Ga Gwamnoni: Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya
- An Wallafa Littafin Xi Jinping Game Da BRI Bugun Shekarar 2023
A farkon makon nan, babban hafsan mayakan kasa na Nijeriya, Lt. General Taoreed Lagbaja ya bayyana cewa akwai dakarun soji fiye da 50,000 da ke ayyukan tsaro daban-daban a sassan kasar nan.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawan Nijeriya, sun bayyana cewar matukar ana son samun nasarar magance matsalolin ‘yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta, sai an samu hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro.
Kamar yadda aka yi tsammani, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ritayar da dukkan hafsoshin sojin kasar da sufeto-janar na ‘yansanda, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro kamar mai ba da shawara kan tsaron kasa da wasu shugabannin hukomomin tsaro da ba na soja ba, wadanda ya gada daga tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
Sabbin nade-naden sun zo da ba-zata inda aka jiyo sunan Mallam Nuhu Ribadu a matsayin Mai Ba wa Shugaban Kasar Shawara Kan Harkokin Tsaron Kasa, wanda kuma shi ne dansanda na farko da aka taba nadawa a wannan mukami a tarihin Nijeriya. Sai kuma Janar C.G Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaro, yayin da, Laftanar Janar T. A Lagbaja ya zama Babban Hafsan Sojin Kasa. sai kuma Rear Admirral E. A Ogalla da aka nada Babban Hafsan Sojojin Ruwa.
Haka nan Tinubu ya nada, ABM H.B Abubakar Babban Hafsan Sojojin Sama, sai kuma Kayode Egbetokun a matsayin Sufeto-Janar na ‘Yansanda. Manjo Janar. EPA Undiandeye a matsayin Babban Hafsan Hukumar Tattara Bayanan Sirri na Soja.
Sabbin shugabannin tsaron da aka nada sun bayyana kudirinsu na fuskantar matsalar tsaron da Nijeriya ke kaka-ni-ka-yi a ciki. Sai dai duk da cewa akwai nasarori da suke samu amma kuma akwai sabbin kalubale da ke kunno kai, kamar dawowar hare-haren boko haram da sauya dabarun ‘yan bindiga da kuma tafka mugun kuskure na jefa wa fararen hula bam daga jami’an tsaro.
- Dawowar ‘yan ta’addan Boko-Haram
Jama’a sun fara bayyana shakku dangane da yadda ake fuskantar barazanar dawowar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a Jihohin Borno da Yobe, a daidai lokacin da ake tsammanin an raka bako; ashe yana labe a bayan gari.
Hakan ya biyo bayan wasu munanan hare-haren da mayakan ke ci gaba da aiwatarwa a wasu sassan jihohin biyu.
A shekarar ta 2023, akwai lokacin da cikin kasa da wata daya, mayakan suka aiwatar da munanan hare-haren da suka jawo salwantar rayuka sama da 50 a Borno, kana suka kashe kimanin 40 a Kauyen Nguro-kayya dake Karamar Hukumar Gaidam a Jihar Yobe. Ko a wannan makon da ake dab da bankwana da shekarar, sun tarwatsa wasu kayayyakin lantarki da suka yi sanadin jefa Borno da Yobe cikin duhu.
- Yunkurin sulhu da ‘yan bindiga da ci gaba da tafka ta’asarsu
Shawarar da tsohon Gwamnan farar hula na farko a Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayar na batun sulhu da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma ya tayar da kura ainun a Nijeriya inda aka yi ta Allah wadai da lamarin.
Ana ganin matukar an yi sulhu da ‘yan bindigar zai zama duk ta’asar da suka yi sun ci bulus kenan. Amma duk da kushen sulhun, sai ga shi wata tawaga da ta tace ministocin tsaro ne daga Abuja suka aiko ta, a boye ta gana da ‘yan bindiga a yankin Katsina don sulhu. Daga bisani Gwamnatin Zamfara ta yi tutsu da lamarin inda ita ma Gwamnatin Katsina ta ce babu hannunta, suka kuma sake jaddada aniyarsu ta yakar ‘yan bindigar ta hanyar kafa dakarun tsaron garuruwa. Katsina ta riga ta kaddamar da nata, yayin da Zamfara ke dab da kamala horas da nata.
Wannan ya sa ‘yan bindigar sun ci gaba da tafka ta’asa a arewa maso yamma inda ko a cikin Disambar nan sun kashe mutane a Zurmi da tsakanin Jibiya da Katsina baya ga sauran kauyuka da suke sace mutane saboda sun ki biyan harajin da suka kakaba musu.
Daruruwan mutanen da ‘yan bindiga ke kashewa a da matukar tayar da hankali a Nijeriya musamman yadda ko a ranar Kirsimeti, suka farmaki wasu garuruwa akalla 15 a Jihar Filato inda rahotanni ke cewa an kashe akalla mutum 160 zuwa lokacin hada wannan rahoton.
- Hare-haren sojoji a kan fararen hula
Harin da sojoji suka kai bisa kuskure kan farar hula da ke taron Mauludi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, a ranar 3 ga Disamban 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 85 ne ya fi daukar hankali a kan wadanda suka auku a baya a shekarar ta 2023.
Masana harkokin tsaro sun dade suna sukar irin sakacin da ake samu a yaki da ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma na ‘yan bindiga a arewa maso yamma, da ke ritsawa da rayukan fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
 A farkon wannan shekarar (ranar 25 ga watan Janairu 2023) an kashe mutum 40 sakamakon harin da jirgin yaki ya kai a kan fararen hula a Jihar Nasarawa, haka kuma a a ranar 5 ga watan Maris 2023 inda mutum uku suka mutu a harin da wani jigin yaki ya kai a kan mutane, daga nan kuma sai harin da jirgin saman sojoji ya kai a ranar 18 ga watan Agusta 2023 inda mutum daya ya mutu.
- Nasarorin da jami’an tsaro suka samu
Shalkwatar rundunar tsaro ta sojin Nijeriya ta rika bayyana nasarorin da dakarunta suke samu na halaka daruruwan ‘yan ta’addar Boko Haram da kuma ‘yan bindiga a sassa daban-daban na kasar nan.
Har ila yau, sun bayar da rahotannin kwato makamai da sauran kayan abinci, babura, abubuwan fashewa shanu daga hannun ‘yan ta’addar. Haka nan sun kwato danyen Mai na sata da kuma Gas na mota wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 259 daga hannun tsagerun yankin Neja Delta.
Bugu da kari, dakarun sojojin Nijeriya sun samu nasarar tarwatsa mafakar kasurguman ‘yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto. Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kyaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojojin sun kara matsa kaimi a yakin da suke da ‘yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma.
Ko a ranar Alhamis ta makon jiya, mai Magana da yawun shalkwatar tsaro ta Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba ya ce cikin mako daya a watan Dismabar nan, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 40 da cafke 191 da kuma ceto mutum 80 da aka sace ana garkuwa da su. Haka nan su ma barayin mai akalla 68 sun shiga hannu.
Hakazalika, kashe kasurgumin dan bindigar nan da aka fi sani da Kachalla a arewa maso yamma wata manuniya ce ga irin nasarorin da jami’an tsaron ke samu.
Duk a shekarar ta 2023, sojojin sun kai samamen shara a kauyukan Dada, Rukudawa, da Dumburum duk a karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara. A cewarsa, yayin wannan samamen, sojoji sun yi musayar wuta da ‘yan bindiga suka nuna musu karfin sanin aiki wanda bisa tilas ‘yan ta’addar suka tsere da raunuka. Sannan dakarun sun hallaka dan bindiga daya a musayar wutar da suka yi.
Karin girma da ritaya
Duk dai a shekarar ta 2023, an yi wasu manyan sojoji akalla 115 ritaya yayin da aka kara wa wasu 214 girma ciki akwai manjo janar 122 da Birgediya Janar. Karin girman ya shafi dakarun ruwa da na sama.