Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar ‘yan wasa guda biyu, Franck Yannick Kessier, wanda kwantiraginsa ya kare a AC Milan a watan jiya da kuma Andreas Christensen daga Chelsea.
Dan wasa Kessie ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2026 haka kuma Barcelona ta sa farashin Yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Camp Nou.
Ranar Laraba 6 ga watan Yuli, Barcelona ta gabatar da Franck Yannick Kessie a matakin dan wasanta kuma an haifi Franck Kessie ranar 19 ga watan Disambar shekarar 1996 a garin Ouragahio da ke Ibory Coast.
Dan wasan mai buga wasa daga tsakiya ko tsaron baya daga tsakiya ya fara wasa a Stella Club d’Adjame ta Ibory Coast daga baya ya koma Atalanta a shekarar 2014 kuma bayan da ya taka rawar gani a kakar wasa ta 2016 zuwa 2017 a Atalanta, daga nan ne AC Milan ta yi zawarcinsa.
Ya koma AC Milan buga wasannin aro a 2017 daga nan ta saye shi a 2019 kan Yuro miliyan 33 kuma tsawon kakar was biyar da Kessie ya yi a Milan ya kara samun gogewa, ya kuma ci kwallaye, ya kuma bayar an zura a raga.
Dan wasan tawagar Ibory Coast ya taimakawa AC Milan ta dauki Serie A a kakar da aka karkare, kofin farko da ta dauka tun bayan kakar wasa 11. Har ila yau, Barcelona ta sanar da daukar dan wasa Andreas Christensen daga Chelsea, bayan da kwantiraginsa shi ma ya kare a Stamford Bridge a karshen watan Yuni kuma Christensen ya amince da kunshin yarjejeniyar.
kaka hudu da saka farashin Yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukarsa, idan wa’adinsa bai kare ba a Camp Nou.
Dan kwallon ya koma Chelsea daga Brondby a shekarar 2012, wanda kaka biyu tsakani ya fara buga wasa a matakin kwararren dan wasa sai dai Chelsea ta bayar da aron dan wasan kaka biyu ga Borussia Monchengladbach, sai dai tun da ya koma Chelsea ya nuna kansa.
Ya buga wa kungiyar wasanni 167 har da 26 da ya yi a kakar da ta wuce da cin kwallo hudu kuma dan kwallon ya lashe Champions League da Europa League da Club World Cup da kuma UEFA Super Cup a wasannin da ya yi wa kungiyar Stamford Bridge.
Haka kuma Chelsea ta yi nasarar cin wasanni 92 a karawar da Christensen ya buga mata sai dai Bayan da Barcelona ta kammala daukar Christensen da Kessie, kungiyar za ta mayar da hankali kan zawarcin Raphinha na Leeds United.
Haka kuma Barcelona na tattaunawa da Ousmane Dembele kan tsawaita zamansa a Camp Nou, bayan da yarjejeniyar dan kwallon tawagar Faransa ta kare a kungiyar kuma tuni dai Manchester United ke ta kokarin ganin ta kammala sayen dan wasan Barcelona, Frenkie de Jong kafin fara kakar bana da za a yi a cikin watan Agusta.