Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kasafin kudin badi (2024) a matsayin Naira tiriliyan 27.5.
Hakan ya zama kari a kan hasashen farko na kasafin da Naira tiriliyan 1.5.
- Sojoji Sun Gargadi Masu Zanga-Zanga A Nasarawa
- Gwamnatin Tarayya Na Kashe Miliyan 3 Kullum Wajen Ciyar da Fursunoni 4,000 – Minista
Ministan kasafin kudi Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan bayan Taron Majalisa Zartarwa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 haka nan ita kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.
Yanzu dai har gwamnatin na shirin mika kasafin ga majalisar dokokin tarayya don amincewa.
Fadar shugaban kasa ta ce a yau Laraba Tinubu zai gabatar da kasafin kudin ga gamayyar Majalisar Dokokin kasar nan.
A zamanin gwamnatin Buhari, kasafin kudin Nijeriya ya dawo aiki daga watan Janairu zuwa Disamba.