Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ci gaba da jan zarenta a sabuwar kakar kwallon kafa ta bana, yayin da ta zazzaga kwallaye bakwar a ragar Real Valladolid a filin wasa na Stadio Companys da ke birnin Barcelona.
Sabon mai horar da ‘yan wasan Barcelona Hansi Flick, ya samu nasara a dukkanin wasanni hudu da ya buga a Laliga, yayin da ya dare teburin gasar da maki 12 da kwallaye 13.
- Shugaban Afirka Ta Tsakiya: Karin Kasashen Afirka Suna Son Zurfafa Hadin Gwiwa Da Sin
- Hanyoyi 7 Na Bunƙasa Kasuwanci A Nijeriya
A wasan wanda aka fara da yammacin yau Asabar, ya matukar kayatarwa tun a mintuna 45 na farko, inda Raphinha, Lewandowski da Kounde suka jefa kwallaye uku.
Bayan dawowa hutun rabin lokaci Raphinha ya sake jefa kwallaye biyu, Dani Olmo daya sai Ferran Torres wanda aka saka daga baya shi ma ya jefa kwallo daya.
A haka wasan ya tashi, inda Barcelona ta ke da kwallaye kwallaye rigis, yayin da Valladolid na nema.