Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta shirya tattaunawa da dan wasan Manchester City, Sergio Aguero, wanda yake shirin barin kungiyar a karshen kakar wasa sakamakon rashin samun damar buga wasanni akai-akai a bana.
Aguero, wanda a kwanakin baya ya samu rashin jituwa da kociyan na Manchester City yana fatan barin kasar Ingila da buga wasa saboda wasu dalilai kuma hakan yasa ake ganin kungiyar Barcelona ce ta dace dashi a wannan lokacin.
A kwanakin baya Guardiola ya ce lallai Manchester City tana bukatar Sergio Aguero da ya koma buga mata wasa saboda a wannan lokacin suna bukatar kasancewarsa a cikin tawagar tasu sakamakon kwarewar da yake da ita.
Rabon da Manchester City ta zama ta daya a teburin gasar Ingila tun ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2019 wanda hakan yasa aka fara hasashen cewa karsashin kungiyar ya fara disashewa a karkashin koyarwar Guardiola.
Rashin Aguero a Manchester City ya bai wa Gabriel Jesus da Kebin de Bruyne da Ferran Torres da kuma Riyad Mahrez daukar alhakin ci wa kungiyar kwallaye kuma daga ranar 22 ga watan Disamba Manchester City ta ci kwallo 20 a wasa bakwai, ba tare da Aguero ba wanda ya zura kwallo 256 a kaka tara da rabi da ya yi a kungiyar.
Tun bayan tafiyar da dan wasa Luis Suares yayi daga Barcelona zuwa Atletico Madrid kungiyar take tsananin bukatar dan wasan gaba mai zura kwallo a raga kuma hakan yasa shugabannin kungiyar suke ganin Aguero zai iya cike musu wannan gurbi.
Yanzu dai abinda ake jira shi ne saka ranar da kungiyar zata gudanar da zaben shugaban gudanarwa wanda hakan ne zai haska akalar da Barcelona zata kalla musamman a sha’anin sababbin ‘yan wasa.