Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni sun taya al’ummar Musul-mi murnar barka da karamar sallah, inda suka bukaci su yi amfani da bukukuwan karamar sallah wajen sadaukar ga kai da addu’on samun ci gaban kasa.
A cikin sanarwar da Shugaba Tinubu ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya taya daukacin Musulmin Nijeriya da ma duniya murnan karamar sallah tare da yin addu’ar Allah ya sa addu’o’i da sadaukarwar da suka yi a lokacin azumin watan Ramadana sun samu sakamako mai kyau daga wurin Allah Madaukakin Sarki.
- PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor Osimhen
- Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku
Karamar sallah tana da matukar mutummanci wanda ke nuna cewa an kawo karshen watan Ramadan, lokaci ne da ke da ake nuna cikakkiyar biyayya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma yin hidima ga Bil’adama.
Kamar yadda shugaban kasa ya jaddada a lokacin buda baki tare da wasu shugabanni a Nijeriya, ya yi kira ga daukacin ‘yan kasar da su hada kai wajan aikin gina kasa.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa darussa, albarka da kuma jin dadin wannan sallah su ci gaba da kasancewa ga jama’a a ko da yaushe tare da yi wa ‘yan Nijeri-ya fatan murnar zagayowar karamar Sallah.
Shi ma gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da amfani da darussa da sadaukarwa da da’a da kuma soyayya da aka koya a cikin watan Ramadan.
Gwamnan ya ce dole ne ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani mai zurfi kan halin da kasar ke ciki.
Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar kammala daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, ya ce, “Ku tuna cewa tawakkali yana da muhimmanci a ci-kin duk abin da kuke yi a lokacin watan Ramadana da kuma bayansa”.
A cewarsa, Musulmai sun kammala gudanar da daya daga cikin wajiban Musulunci na azumi tsawon wata guda tare da yin addu’o’i da sauran nau’ikan ibada.
Ya kuma bukaci dukkan al’ummar Musulmai da su yi koyi da darasin da suka koya a cikin watan Ramadan ta hanyar sadaukarwa, sadaka ga mabukata da kuma nu-na soyayya ga juna.
Shi ma takwaran sa na Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar karamar sallah wanda ya kawo karshen azumin wa-tan Ramadan.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwam-nan, Rafiu Ajakaye, ya taya jagoran shugaban majalisar sarakunan jihar, Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, murnar kammala azumin wa-tan azumi.
Ya bukaci al’ummar Musulmi da su dauki darasi ga ayyuka masu kyau na wannan wata Ramadan, wadanda suka hada da sadaka, kaurace wa munanan dabi’u da addu’o’i.
AbdulRazak ya kuma bukaci al’umma da su hada kai wajen aikata alkhairai tare da nisantar duk wani abu da zai iya cinye ladan azuminsu, ko kuma ayar tambaya ga ikilasinsu na ibada.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni sh ma ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Buni ya hori Musulmi da su kasance masu kaunar juna tare da kara kaimi wajen kyautata wa makwabtansu.
A cewarsa, “Yayin da muke gudanar da bukukuwan karamar sallah, wanda ya nuna kawo karshen azumin watan Ramadana na tsawon wata daya ana gudanar da ibada, ina kira a gare mu da mu dauki darussa na sadaukarwa, jin kai da ake nunawa a lokacin azumin watan Ramadan.
“Na yaba da gagarumin shirin ciyarwa da gwamnatoci, daidaikun mutane, da kungiyoyi, kamfanoni suka bayarwa ga marayu, iyalai marasa galihu da kuma mu-tane masu rauni a cikin al’umma. Ya kamata a karfafa hakan ko da bayan Rama-dan,” in ji Buni.
A cikin sakon barka da sallah da daraktan yada labarai na gwamnan Jihar Filato, Gyang Bere ya sanya wa hannu, gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya taya al’ummar Musulmi murna karamar sallah tare da yaba wa sadaukarwar da suka yi wajen jin tsoron Allah.
Sannan ya kwadaitar da su da su rungumi darasin da aka koya a Ramadan da suka hada da kwadaitar da kyawawan dabi’u, tawali’u, kyautatawa da ciyarwa ga marasa galihu, su ci gaba har bayan watan Ramadan.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Gwamnan Jihar Bayelsa, Dan-iel Alabrah ya fitar, ya ce azumi na daya daga cikin ginshikan addinin Musulunci, watan Ramadan na da matukar muhimmanci wajen raya kyawawan halaye ga kowane Musulmi na kwarai.
Gwamnan Jihar Inugu, Dakta Peter Mbah, ya taya al’ummar Musulmin jihar da kasa baki daya murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Ya bukace su da su ci gaba da amfani da darussa da suka koya daga watan Rama-dan da suka hada da kyawawan dabi’u na soyayya, hakuri da juriya domin ciyar da jihar da Nijeriya gaba daya.
Gwamnan Jihar Kuros Riba, Bassey Otu, ya bukaci al’ummar Musulmi a jihar da ma kasar nan da su nuna hakikanin zaman lafiya da soyayya a cikin mu’amalarsu ta yau da kullum da mabiya addinai daban-daban, inda ya ce addinin Musulunci addinin zaman lafiya ya kore duk wani tashin hankali kowane iri.
Gwamnan wanda ya taya al’ummar Musulmi murnar samun nasarar kammala azumin watan Ramadan na bana, ya bukace su da su yi amfani da darussan da su-ka koya a cikin azumin watan Ramadan domin kawo sakamako mai kyau ga ma-kwabta da sauran al’umma.
Hakazalika, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taya al’ummar Musulmin murnar kammala azumin watan Ramadan.
A wata sanarwar manema labarai da ofishin Atiku ya fitar, ya ce ya kamata a ci gaba da yin koyi da darussan azumin watan Ramadan.
Har ila yau, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Mista Peter Obi, ya bukaci Musulmin Nijeriya da su yi amfani da bikin Sallah wajen neman taimakon Allah kan daina zubar da jini a Nijeriya.
Obi ya ce ya kamata jama’a su yi amfani da bukukuwan karamin sallah ta bana wajen samar da hadin kai tare da sadaukar da kansu ga kyawawan halaye na soyayya da kishin kasa domin ci gaban kaasa.
Kungiyar kiristoci ta NIjeriya (CAN) ta yi kira ga shugabannin siyasa a dukkan ma-takai na gwamnati da su hadin kai wajen samun zaman lafiya ta hanyar sanya ky-awawan dabi’u da shugabanci na gari wajen yi wa kasa hidima.
Shugaban kungiyar CAN, Archbishop Daniel Okoh, wanda ya yi wannan kiran a cikin sakonsa na barka da Sallah ga al’ummar Musulman Nijeriya. Ya ce kyakkya-wan shugabanci da gaskiya da rikon amana da rashin son kai na da matukar mu-himmanci wajen tafiyar da Nijeriya tafarkin ci gaba mai dorewa da hadin kai.