Bashi Hanji Ne: Yaushe Nijeriya Za Ta Tsaya Kan Kafafunta? 

Bankuna

Duk da bashi hanji ne a cikin kusan kowace kasa a duniya, sai dai kowace kasa da irin nata yanayi ko manufar yin karamar murya da neman bashin, wanda tarayyar Nijeriya ta na daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna a hanyar karbar bashi daga kasashen duniya don gudanar da manyan ayyukan ci gaban kasa da makamantan su, wannan al’amari ya dade yana ci wa masana da manazarta tuwo a kwarya tare da bayyana fargabar abinda hakan zai jawo wa kasar a idon duniya.

 

A kasafin kudin 2021 da gwamnatin tarayya ta gabatar a gaban majalisa na naira tiriliyan 13.8, wanda ya kunshi gibin kimanin kaso 30 cikin dari na kasafin, wanda yayi daidai da naira tiriliyan 5.6 a matsayin dole sai an hada da bashi sannan a iya aiwatar dashi. Yayin da bayan amincewa da kasafin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar ta bashi damar karbo bashin naira tiriliyan 2.3 (Dalar Amurka 6.18 ) don samun damar aiwatar da sashen kasafin 2021.

 

Wannan dogon lokaci da gwamnatin Nijeriya ta dauka wajen nacewar ci gaba da kutsa kai a manyan kasashen duniya wajen neman bashin ya na kokarin mayar da hannun agogo baya da jefa kasar shiga igiyoyin bashi, musamman ta la’akari da kallon da cibiyoyin harkokin kudin wasu kasashen duniya, irin su World Bank, African Debelopment Bank, French Debelopment Agency, Islamic Debelopment Bank, China EDIM Bank, China Debelopment Bank, European Inbestment Bank, European ECA, KFW, IPED, AFC, India EDIM Bank, International Fund for Agricultural Debelopment da makamantan su da dama.

 

Bugu da kari, ko a makon da ya gabata, shugaban kasa Buhari ya sake garzaya wa zauren majalisar tarayya tare da neman yan majalisar su sake mashi damar ciwo bashi daga kasar waje, inda ya bayar da hujjar cewa don bai wa gwamnatin tarayya zarafin gudanar da wasu manyan ayyuka, wadanda suka hada da inganta hanyoyin sufuri, kiwon lafiya da ilimi da sauran su. Wannan ya jawo masana dora ayar tambaya kan cewa: shin wane tasiri sauran basusukan da aka ciwo a shekaru shidan da suka gabata ya yi a ci gaban tattalin arzikin Nijeriya? Sannan kuma yan Nijeriya da dama basu mamakin irin yadda bangaren majalisa kan yi biris da nauyin da ya hau kansa na bincikar yadda aka aiwatar da bashin da aka karbo a baya ba, wanda wasu na da ra’ayin cewa da walakin- domin mafi yawan yan majalisar yan amshin shata ne, basu da kuzarin da zasu bi bahasin yadda abubuwan ke gudana.

 

Wanda ana iya cewa kusan kasar ta dogara da cin bashi wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaban kasa, wanda ya zama tamkar kawanya a hannu; kafin a biya wannan bashin an garzaya neman wani? Sannan a watanni shidda na farkon shekarar 2020 ana bin gwamnatin tarayya ruwa na bashin naira tiriliyan 1.57. Haka kuma da zarar bashi ya na karuwa wajen biya, zai jawo karin haraji, wanda kamata ya yi gwamnati ta dena cin basussuka haka barkatai- me ye abin cin bashi wajen gina layukan dogo, wutar lantarki ko gina filin jirgin sama? Ya dace gwamnati ta bai wa yan kasuwa dama su shigo don bayar da muhimmiyar gudumawa a fannin ci gaban tattalin arzikin kasa, musamman irin su gina layukan dogo. Wanda a manyan kasaahen da suka ci gaba, kofofin su a bude suke wajen tafiya kafada da kafada da yan kasuwa masu zaman kansu hatta a harkoki irin su kiwon lafiya, ilimi tare da sauran abubuwan habaka jin dadin yan kasa, amma a Nijeriya ba haka abin yake ba, gwamnati ce ke uwa da makarbiya a kowanne sashe, hatta bangarorin da suka kebanci yan kasuwa da zuba jari ita take yin kane-kane a kai.

 

A hannu guda kuma, kasashen da suka ci gaba suna kokari wajen habaka tsarin da ake kira “Build Operate and Transfer” (BOT) wajen gudanar da wasu manyan ayyuka a kasa ta hanyar amfani da kananan masana’antu na cikin kasa ko daga waje, wanda idan da gaske ne kasar China tana kaunar Nijeriya, me zai hana ta kulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya a karkashin tsarin BOT wajen gina layin dogo, wutar lantarki ko gina filayen jiragen sama su bamu a matsayin bashi.

 

Abin a yaba ne idan gwamnatin tarayya za ta samu wannan alfarma daga irin wannan tsarin bashi wajen aiwatar da wasu manyan ayyukan ci gaban kasa wadanda suke da alaka da tsarin yan kasuwa Su gudanar dasu, wanda ko shakka babu yan kasa zasu ci gajiyar su sosai, irin su: inganta Nigerian Railway, Abuja Light Rail; akin sadarwa na zamani na ICT, Airport Terminal Edpansion Project (a Abuja, Kano, Lagos da Patakwal ), aikin samar da wutar lantarki na Zungeru Hydroelectric, 40 Parboiled Rice Processing Plants, inganta aikin layin dogo na Lagos zuwa Ibadan, aikin samar da wuta na Mambilla, tare da sake gina tashar NTA da makamantan su.

 

Har wala yau kuma, yan Nijeriya ba zasu taba gamsuwa da yanayin ka’idoji da yarjejeniyar da China ke gindaya wa wajen bayar da bashi ba, saboda yadda suke cike cutarwa, wanda tsakanin shekarar 2010 zuwa 31 ga watan Maris na 2020, irin wadannan basussuka guda 11 ne gwamnatin tarayya ta karbo daga bankin China “EDIM Bank”. Wanda mafi yawan wadannan bashin sun ta’llaka ne bisa yarjejeniyar bayar dasu ne ta hanyar su ne kadai zasu gudanar da kwangilar ayyukan, illa iyaka kawai su aiwatar dasu iya son ransu kana daga bisani a biya bashin, sannan ga aringizon ‘ruwa’ idan sun dauki dogon lokaci ba a biya ba.

 

Wanda a wani bashin da gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar karba daga hannun China shi ne na gina layin dogo tsakanin Lagos zuwa Ibadan, wanda gwamnatin China ta yanke masa farashi dala miliyan 500. Sannan kuma a haka aka kulla yarjejeniyar gina shi ta hanyar kamfanin kasar China, wanda suka tsara su zasu shigo da dukan kaya da ma’aikatan da zasu yi amfani dasu a aikin, face kawai sun dauki yan Nijeriya a matsayin lebarori. Yayin da karbar wannan bashin ya bai wa kasar China cikakkiyar damar shigo da kaya zuwa Nijeriya.

 

A lokuta da dama hukumar bayar da lamuni ta duniya (IMF) ta tsaya kai da fata tare da yi wa Nijeriya da sauran kasashen masu tasowa gargadin kar suyi gigin huldar bashi China inda ta bayyana hakan a matsayin babban hadari kuma babbar matsala. Ta kara da cewa duk kasar da ta shiga komar China a matsayin karbar bashi, to kuwa sai dan buzunta, domin cikin kankanin lokaci kasar zata durkushe tattalin arzikinta ya shiga rudani, wanda idan bata yi sa’a ba, kan ta farga sai dai a bayar da labarinta.

   

 

 

Exit mobile version