Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatocin Jihohin Sakkwato da Zamfara sun kasance a cikin duhu bakidaya a yayin da Hukumar Wutar Lantarki ta Kaduna (KEDCO) ta tsinke layukan wutar a dalilin dimbin bashi.
Kamfanin KEDCO ya bayyana cewar ba ya da wani zabi face daukar matakin yanke wutar bayan cikar wa’adin makwanni uku da suka baiwa Gwamnatocin domin su biya tarin bashin da kamfanin ke bin su ko su saka su a duhu.
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki BaÂ
- An Raba Wa Jami’an Tsaro Na NSCDC 7 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe Cakin Banki Da Guraben Aiki
Shugaban sashen Yada Labarai na KEDCO Abdul’aziz Abdallah a sanarwar da ya fitar makon jiya ya bayyana cewar kamfanin na bin Gwamnatin Jihar Sakkwato tsabar kudi naira biliyan 1, 496, 313, 156 a yayin da Gwamnatin Zamfara ke rike da bashin kamfanin na naira biliyan 1, 040, 506, 740 daga watan Disamba 2022.
Yanke layukan ya haifar da tarin illoli da dama a Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatocin biyu kasancewar ayyukan yau da kullum na gudanar da ofisoshi da dama sun tsaya, wasu kuma ba su tafiya yadda ya kamata.
A wasu ma’aikatu ba su da zabi face amfani da injinin janareta domin haskaka ma’aikatun da kuma aiwatar da ayyukan da suka wajaba a gare su.
Sanarwar ta bayyana cewar yanke wutar shine mataki na karshe da za su iya dauka musamman saboda rashin biyan bashin wanda KEDCO ta bayyana cewar ba wai hakan na kawo masu cikas wajen aiwatar da ayyukan su ne kawai ba, yana kuma zamar masu matukar wahala wajen sauke nauyin da ke kan su na baiwa al’umma haske da kuma samun ribar da za su kara inganta ayyukan su.
“Abin damuwa ne yadda Gwamnatin Zamfara ta kasa biyan kudin wuta a tsawon watanni 12 da suka gabata a yayin da Jihar Sakkwato ta kasa biyan wuta na tsawon watanni hudu.”
Bayanin ya nuna cewar Hukumar KEDCO ta dauki matakin bayar sanar da Gwamnatocin bukatar biyan basukan da kuma notis na karshe bayan da dukkanin alkawulan da suka dauka na biyan kudaden ya faskara duk da an yi ta tunatarwa.
Kamfanin na KEDCO ya bayyana cewar ya wajaba ga kamfanin su rika biyan kashi 100 na wutar da suke karba da na gudanarwa wanda akwai hukunci idan suka saba wanda a kan hakan kamfanin ya ce wannan dalilin ne ya sa suke fadi tashi a kowane wata amma abin kan faskara saboda karanci, rashin biya da biyan wuta ba bisa ka’ida ba.
“Muna bayar da tabbacin cewar a shirye muke mu mayar da hasken wuta a ma’aikatun Gwamnatocin biyu da muka yanke idan aka dauki matakan da ya kamata na biyan dadadden bashin da kuma tabbacin ci-gaba da biyan wuta yadda ya kamata a cikin lokaci.” In ji kamfanin.