Sulaiman Bala Idris" />

Batun Aika Sakamakon Zaben 2019 Ta Fallayen Takardu

Dududu bai kai wata guda kacal a gudanar da zaben 2019 mai zuwa, amma ga dukkanin alamu za a aiwatar da zaben ne ba tare da na’ura mai aika sakamakon zaben kai tsaye daga rumfunan zabe ba. Kamar yadda bincike ya nuna, rashin yin amfani da wannan na’ura babu shakka ya cusguna wa mafi yawan ‘yan Nijeriya don kuwa ba haka suka yi tsammani ba.
Idan za mu iya tunawa, Hukumar zabe ta kasa (INEC), ta fara gwaje-gwajen wannan na’ura tun a shekarar 2014, kawo yanzu ya kamata a ce Hukumar ta samu cikakkiyar kwarewa wajen ci gaba da sarrafa wannan na’ura kamar yadda ‘yan Nijeiya suka kwallafa rai suka kuma kagu su ga an yi amfani da ita a zaben mai zuwa.
Kazalika, Hukumar zaben, ta jima tana yin gwajin wannan na’ura don ganin ta saukaka hanyar bayyana sakamakon zabe kai tsaye tun daga rumfunan zabe zuwa wajen tattara sakamakon zaben na jiha. Hukumar ta bijiro da wannan sabuwar hanya ne don magance magudin zabe, aringizo da sauran wuru-wurun zabe da kuma tabbatar da samun sahihin zaben a kasa baki daya.
A kwana kwanan nan ne Hukumar ta sake tabbatarwa da masu niyyar kada kuri’a a zaben 2019 mai zuwa cewa, babu wanda kuri’arsa ba za ta yi tasiri ba har in ya kada ta a lokacin zabe. Haka zalika, duk wanda ba shi da kuri’ar ya tabbata ya je ya yi rajista, wadanda kuma suka yi rajistar ba su karba ba su tabbata sun je sun karba. Babu shakka wannan kira ya yi matukar tasiri a kan Milyoyin ‘yan Nijeriya don kuwa sun amsa kiran nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
An yi tsammanin Hukumar INEC za ta mayar da hankali wajen aiwatar ko amfani da sabuwar hanyar aika sakamakon zaben kai tsaye daga rumfunan zaben zuwa babban ofishin tattara sakamako na INEC. Mafi rinjayen ‘yan Nijeriya sun tafi a kan cewa Hukuma INEC ta kasa za ta yi amfani da wannan sabuwar na’ura kafin zaben 2019 mai zuwa.
Har ila yau, amfani da wannan sabuwar hanya ko na’ura za ta ragewa ‘yan siyasa karsashi ko yin katabus musamman a wajen yin magudin zabe ko canza alkaluma ko kuma sace akwatunan zaben da tuni ya rigaya ya zama ruwan dare a wajen su. Yin amfani da na’urorin zamani wajen bayyana sakamakon zabe, ko shakka babu zai rage radadi ko damuwa wajen daukar lokaci kafin sanar da sakamakon zabe, sannan yin hakan ba zai bawa masu saurin yada labaran kanzon kurege damar yada ko bayyana sakamakon karya ba musamman a zaurukan sada zumunta da ake yin amfani da su na yau da kullum ba.
Sa’annan bayyana sakamakon zabubbuka ta hanyar na’urar zamani na rage afkuwar magudi da ‘yan takarkaru ke yi a boye ko a fili ba. Haka nan, akwai koke-koken mutane da ‘yan Majalisun tarayya suka shigar da ‘yan jaridu da kuma sauran kungiyoyin al’umma cewa, dokar da za ta tilastawa Hukumar zabe yin amfani da wannnan na’ura har yanzu ba a rattaba mata hannu ba.
Koda yake, dokar zaben ta fayyace yadda za a bayyana sakamakon zaben, amma fa ba ta hanyar yin amfani da sabuwar na’urar zamanin ba. Idan ana so a tilasta yin amfani da sabuwar hanyar bayyana sakamakon zaben, dole sai an yi wa dokar garanbawul, idan kuma ba haka ba koda an yi amfani da sabuwar na’urar za a iya kalubalantar ta a Kotu.
Muna kara kira ga Humar zabe ta kasa, ta tabbata ta dora a kan tarihin da ta bari a zaben 2015. Kazalika, akwai bukatar Hukumar INEC din da Hukumomin tsaro da Sarakuna da sauran duk masu fada a ji, su tabbatar an yi zabe na gaskiya ba tare da magudi ko cin zarafin masu yin zaben ba a duk fadin wannan kasa baki daya.
Haka nan, bayyana sakamakon zabuka ta tsohuwar hanya fallayen takardu kamar yadda aka saba a baya, ba karamin koma baya zai kawowa Hukuma INEC din ba, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da ta samu a zabukan da aka aiwatar a shekarun baya da suka gabata. Amma duk da rashin yin amfani da sabuwar hanyar bayyana sakamakon zaben, hakan bai hana Shugaban kasa mai ci yanzu samun nasarar lashe zabensa ba, da taimakon masu sanya ido na cikin gida da kuma kasashen waje inda aka yi nasarar samun sahihin zabe mai kuma cike da dinbin tarihi a yankunan Afrika baki daya.
A karshe muna sake kira ga Hukumomin da al’amarin zabe ya shafa, su tabbata su kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, babu wani daga waje ko cikin gida da zai yi musu katsalandan a kan harkokinsu na zabe. Sannan wajibi ne masu ruwa da tsaki su jajirce wajen ganin an tabbatarwa da talakawa abinda suka zaba musamman wajen bayyana sakamakon zabe na gaskiya a duk fadin kasa baki daya.

Exit mobile version