A yayin da Shugaba Tinubu ya daura damarar yaki da ta’addanci domin cika alkawarin da ya daukar wa ‘yan Nijeriya na kawo karshen matsalar tsaro, tsohon Gwamnan farar hula na farko a Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayyana cewar sasantawa ne kawai mafitar shawo kan ta’addancin.
Yarima wanda ya kaddamar da shari’ar Musulunci a Zamfara a shekarar 2000, ya bayyana wa Shugaba Tinubu cewar sasantawa da ‘yan ta’addan shi ne zai kawo karshen ayyukan ta’addanci a Zamfara da sauran Jihohin Arewa- Maso- Yamma da lamarin ya yi kamari.
- Kamfanin Meta Mamallakin Facebook Ya Yi Wa Twitter Kishiya
- Dalilin Da Ya Sa Nake Shiga Sha’anin Gwamnatin Kano -Kwankwaso
Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da Shugaban Kasa a Abuja a farkon makon nan. A cewarsa zaman sulhu da ‘yan bindigar shi ne zai kawo zaman lafiya a yankin Arewa.
Yariman Bakura ya bayyana cewar sulhun da yake bukatar a yi kwatankwaci ne da irin shirin afuwar da Shugaba Umaru ‘Yar’Adua ya yi da ‘yan ta’addan yankin Neja- Delta wanda a cewarsa ya haifar da da mai ido.
Wakilin mu ya labarto cewar a shekarar 2009, Shugaba ‘Yar’Adua ya aminta da sulhu da ‘yan ta’addan yankin Neja- Delta da ke da albarkatun mai domin kawo karshen satar danyen mai da garkuwa da ma’aikatan mai.
Shirin sulhu da ‘yan ta’addan Neja- Delta ya hada da horas da su abubuwa da dama kan harkokin mai tare da ba su ayyukan yi tare da kudin alawus a kowane wata ga wasu daga cikin tsofaffin tsagerun. Shirin wanda ya ci gwamnati tsabar biliyoyin kudi a kowace shekara, ya dore a gwamnatocin da suka biyo baya.
Duk da cewar shirin afuwar ya haifar da bunkasar hako mai da raguwar garkuwa da mutane a yankin, amma afuwar ba ta kawo karshen ta’addanci ba domin tsagerun da dama dauke da miyagun makamai sun ci gaba da ta’asa ta yadda satar man ta ci gaba da wanzuwa.
Rahotanni a yau sun nuna yawaitar ayyukan ta’addanci a Arewa- Maso-Yamma a baya- bayan nan sun haura ta’addancin da ke faruwa daga tsagerun yankin Neje- Delta.
‘Yan bindigar da ke addabar Arewa- Maso- Yamma da Arewa- ta Tsakiya sun samu galabar tarwatsa garuruwa da dama, kashe dimbin jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba tare da garkuwa da dimbin jama’a domin karbar kudin fansa. A haka a yayin da miliyoyin jama’a suka rasa rayukansu, dubban daruruwa sun rasa dukiyoyinsu, haka ma dubban daruruwan jama’a sun zama marayu kamar yadda dubban daruruwan mata suka zama zawarawa a yayin da miliyoyi da dama suka zama ‘yan gudun hijira.
Duk da hobbasa da kwazon da gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro ke yi a yankin, ‘yan ta’addan sun ci gaba da cin karensu ba babbaka ta hanyar kai farmaki a garuruwan suna kisan jama’a da dama tare da garkuwa da mutane ciki har da matafiya.
“Wadannan mutanen ‘yan Nijeriya ne kuma sojoji da sauran jami’an tsaro suna iya kawo karshen wannan ta’addancin idan har aka ba su dama da dukkanin abin da suke bukata.” In ji Yarima.
Shirin afuwa da Yarima ke bukatar a yi da ‘yan ta’addan ba sabo ba ne a yankin domin kuwa gwamnatocin jihohi sun jagoranci sulhu da ‘yan bindigar a baya amma kuma hakar ba ta cimma ruwa ba.
A 2014, tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari ya yi wa ‘yan ta’addan afuwa domin ganin an samu kwanciyar hankali a jihar. Haka ma a shekarar 2016 tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Masari ya aminta da yi wa ‘yan ta’addan afuwa kamar yadda a 2019 tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle shi ma ya yi wa ‘yan ta’addan afuwa duka da zummar su ajiye makamai domin tabbatar da zaman lafiya amma duka bukata ba ta biya ba.
A yayin da lamarin ya kara ta’azzara a shekarar 2021 ba tare da sassauci ba, ‘yan majalisar Tarayya daga Zamfara sun gabatar da bukata ga Shugaba Muhammadu Buhari kan ya yi wa tubabbun ‘yan ta’addar afuwa a matsayin daya daga cikin hanyoyin kawo karshen matsalar, bukatar da shugaban ya sa kafa ya yi fatali da ita.
Yarima ya bayyana cewar talauci da jahilci su ne silar ta’addancin, don haka a cewarsa yana ganin shirin gyara hali zai yi matukar tasiri domin dawowa da su a cikin al’umma. A cewarsa idan aka ilmantar da su aka kuma kawar masu da fatara za a ga alfanu.
Ya ce tattaunawa na daga cikin muhimman ayyukan gwamnati don haka ya dace a aiwatar da hakan gabanin amfani da kakkarfan karfin soji domin yakar ‘yan ta’addan.
A yayin da yake bayar da misali a tarihance, tsohon Gwamnan ya bayyana cewar manyan yake- yaken da suka shiga cikin kundin tarihin duniya kamar yakin duniya na I da yakin duniya na II duka an kawo karshensu ne ta hanyar sasantawa.
A yayin da yake amsa tambaya kan mummunar aika- aikar da ‘yan ta’addan suka aikata da kuncin da suka jefa al’umma, Yarima ya bayyana cewar ya bayar da shawarar ne domin kawo karshen duka rikice- rikicen da ke faruwa a Nijeriya ba wai ‘yan ta’adda kawai ba.
Ya ce yana da matukar muhimmanci a bai wa ‘yan Nijeriya damar tuba, a gyara halinsu a kuma dawo da su a cikin al’umma. Ya ce yana da tabbacin gwamnati za ta iya domin ta na da dama da goyon bayan shawo kan matsalolin tsaro idan har tattunawa ba ta yi wu ba.
…Sulhu Ba Mafita Ba Ne -Majalisar Matasan Arewa
A yayin da Yarima ke ganin sulhu da ‘yan ta’adda shi ne mafita, a nata bangaren Majalisar Matasan Arewa ta fito fili ta bayyana cewar ko kadan ba ta goyon bayan shawarar da tsohon Gwamnan Zamfara ya bai wa Shugaba Tinubu kan sasantawa da ‘yan bindigar da ke kisan al’umma ba kakkautawa.
Majalisar ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta jaraba wasu hanyoyin domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Arewa da sauran sassan kasa maimakon sasantawa.
A sanarwar da Kakakin Majalisar, Muhammad Danlami ya Sanya wa hannu ta bayyana cewar ko kadan ba ta yadda shawarar tsohon Gwamnan Zamfara, Ahmad Yarima za ta kawo karshen matsalar ba.
Majalisar ta ce ba ta aminta da shawarar Yarima ba ne domin sasantawa ba matakin sulhu ba ne mai dorewa ga kalubalen sha’anin tsaro a yankin don haka suka bukaci a yi amfani da wasu hanyoyin domin kawar da ta’addanci amma ba a matakin sulhu ba.
A ra’ayin itta Majalisar ta bayyana cewar amfani da karfin soji a bisa ga tanadin doka wajen kakkabe ayyukan ta’addanci shi ne babbar mafitar shawo kan matsalar.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar a shekarar 2021, fitaccen Malamin Addini a Kaduna, Sheikh Ahmad Gummi ma ya fito fili ya bai wa Gwamnatin Tarayya shawarar sasantawa da ‘yan ta’addan wanda a ganinsa shi ne maslaha ga kawo karshen matsalar da dorewar zaman lafiya a Nijeriya.
Malamin wanda a wancan lokacin ya rika ziyarar sansani daban- daban na ‘yan ta’addan ya bayyana cewar amfani da karfin soji wajen shawo kan matsalar ba zai haifar da da mai ido ba.
Tuni dai mabambantan al’umma suka rika bayyana ra’ayoyinsu kan aiwatar da sulhu da ‘yan ta’addar ko akasin hakan ta yadda mafi yawan jama’a ke da ra’ayin ko kadan bai dace a sasanta da makasan ba, maimakon hakan suna ganin idan har gwamnati da gaske take yi, to tana da karfin soji da cikakken ikon kakkabe duk wasu ayyukan ta’addanci a Arewaci da Kudancin Kasar nan.
Har ila yau, ya rage ga sabbin shugabannin rundunonin tsaro da aka nada su dora batun sake yin sulhu da yan bindigar a sikeli su gani, ina ya fi kamata a karkata.