Bayan faduwar ba zato ba tsammani biyo bayan cire tallafin man fetur, gwamnatin yanzu da ta mamaye Aso-Rock, a tsarin da ya yi kama da mai neman gudunmawar kashe gobara, ta yanke shawarar kaddamar da shiri daya bayan daya wanda muke fatan zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya a bangarori daban-daban. Wadannan shirye-shiryen, sun hada da raba abubuwan jin dadi, raba shinkafa, tallafin kudi, zuwa damar samun rancen kudi, zuwa horo da sauransu.
Amma kamar kowane shiri na wannan gwamnatin, su zo da nasu fa’idoji da abubuwan da zasu iya haifar da koma baya.
- ‘Yan Majalisar Tarayya 29 Da Suka Mutu A Kan Kujerunsu Cikin Shekara 9
- Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa ‘Yan Kasuwa Wata Guda Su Sauke Farashin Kayayyakin Masarufi
Anan za mu binciki guda 11 don sanin ko suna nuni ne da sadaukar war gwamnati ko labulen taga ce ko kuma rudu ne kawai?
Bari Mu Nutse Cikin Shirye-Shiryen Guda 11
Tsarin Lamunin Dalibai:
Asusun ba da Lamuni na Ilimi na Nijeriya (NELFUND) yana samun kudade ne daga Hadaddiyar Asusun Gwammnatin Tarayya da kuma kudin da aka kwato daga hannun azzaluman kasa.
Shirin na nufin bayar da lamuni marar riba ga daliban da ke neman ilimin jami’a. Wannan shiri dai ya samo asali ne daga sashe na 18 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya samar da damammakin samun ilimi na boko da kuma na yau da kullun a matsayin hanyar karfafawa ‘yan kasa da bunkasa ci gaban kasa.
A matsayin mafita ga dalibai, zai yi kyau a ziyar ci shafin- http://nelf.gob.ng
Shirin CNG na Shugaban kasa: Wannan canjin fasalin motoci zuwa anfani da iskar Gas (CNG) ne, anan gwamnati ta yi niyyar zuwa rancen kudi dalar amurka USD250m (daidai da NGN397.5b). Ma’aikatar Kudi, da na Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, da na Albarkatun Man Fetur, da Ma’aikatar kwadago, da na Sufuri ne za su gudanar da shirin.
Shirin na neman inganta amfani da iskar gas a matsayin mai tsabta, mafi araha maimakon man fetur. Wannan ya yi dai-dai da kundin tsarin mulki na samun yanayi mai kyau a karkashin sashe na 20.
Tsarin zai yi canjin kyauta ga membobin kungiyoyin sufuri da yanke farashin kashi 50% ga masu aikin abun hawa na haya (wato ride-share a turance). Domin cin gajiya, sai a ziyarci shafin https://pci.gob.ng
Wani hanzari, mene ne makomar wadanda ba su cikin wannan rukuni na cancanta?
Kamfanin Ba Da Lamuni ga Ma’aikata: Hukumar ba da lamuni ta Nijeriya (CrediCorp) na karkashin ma’aikatar kudi ta tarayya kuma tana da niyyar kiwon kusan ma’aikata miliyan 40 na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu don su kara yawan amfanin da bashi domin bunkasa sayan abun masarufi na yau da kullun. Sashi na 16 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya umurci gwamnati ta inganta tattalin arzikin dukkan ‘yan kasa.
A matsayin shirin da zai haifar da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, zai dace a ziyarci shafin https://credicorp.ng
Sai dai abin mamaki a nan shi ne, su kuma sauran ‘yan Nijeriya miliyan 180 da suka rage wa’anda basu aikin gwamnati ko aikin blue-collar mece ce makomar su a cikin wannan tsari?
Shirin Kamfanoni na Dijital da Kirkire-Kirkire (iDiCE): Shirin wanda Bankin masana’antu ke gudanarwa, yana tallafawa ‘yan kasuwa na dijital da kere-kere da kudade da albarkatu, yana baiwa matasa damar yin amfani da basirarsu. Yana da goyon bayan sashe na 17 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya ba da umarnin tabbatar da adalci na zamantakewa, inganta rayuwar ‘yan kasa, da magance matsalolin da suka shafi kiwon lafiya, ilimi, da jin dadin jama’a.
Saboda shirin ya kunshi lamuni zai kyautatu a ziyarci shafin- https://boi.ng/iDiCE
Shirin Inganta Kwaraiwar masu Aiki (SUPA): Hakkin gudanarwan ya na hanun asusun horar da ma’aikatan masana’antu (ITF) ne. Shirin yana mai da hankali kan habaka kwarewar masu sana’a, ta yadda za a habaka dogaro da kai da kasuwanci. Sashi na 16 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi kira da a samar da ci gaban kasa.
A ziyaraci shafin https://SUPA.itf.gob.ng domin cin gajiyan shirin.
Zauren Koyar da Matasan Nijeriya (NIYA): Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Tarayya ne za ta gudanar da shi, kuma za ta hada da nasiha da horar da matasan Nijeriya. Hakan ya yi daidai da sashe na 17 na kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda ya wajabta wa gwamnati tabbatar da ci gaban matasa.
Ziyartan shafin https://NIYA.ng zai dace don ganin abubuwan da su kace za su yi.
Shirin Fitar da Hazakar Matasa na Kasa (NATEP): Ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari za ta gudanar da wannan shirin. Kuma a zahiri, ya kunshi horo. Shirin na nufin fitar da hazakar matasan Nijeriya a fagen wasanni, fasaha da al’adu zuwa kasashen waje. Shirin ya yi daidai da sashe na 17, manufofin zamantakewa na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya ba da umarnin tabbatar da adalci na zamantakewa, inganta rayuwar jama’a, da raya al’adu da dai sauransu.
Ga wadanda ke son yin JAPA, ziyartar shafin http://natep.gob.ng ya zama tilas.
Shirin Bada Lamuni ga Kananan ‘yan Kasuwa: Wannan tsarin Bankin Masana’antu ne za ta gudanar,kuma zai ba da taimako na kudi ga kananan ‘yan kasuwa. Zai kuma karfafa ci gaban tattalin arziki da kuma samar da aiki. Sashe na 16, makasudin tattalin arziki, na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ta goyi bayan wannan tsarin, inda ta tabarta da rarraba wadata, da walwala daidai tsakanin ‘ yan kasa domin samun kwanciyar hankali.
Ziyartar shafin https://boi.ng/micro-business ya dace a wannan gabar.
Tsarin Ba da Lamuni na Sayen Gida ko Matsuguni: Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya (FHA) ce ke kula da wannan. Manufar ita ce samar da gidaje masu rahusa ga ‘yan Nijeriya, tare da tallafawa. Kowane dan Nijeriya na da hakkin samun isasshen matsuguni kamar yadda yake kunshe a cikin sashe na 16, manufofin tattalin arziki, na kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya jaddada daidaiton wajen rarraba dukiya da albarkatun kasa a tsakanin ‘yan kasa.
Yayin da shirin ke magance wata muhimmiyar bukata, shirin na ma’aikata ne masu asusun ajiyar siyan gidaje kawai (wato National Housing Fund).
Abun tambaya a nan, mece ce makomar ‘yan Nijeriya da ba su da aikin yi? Shin gidajen suna da araha kuma suna da inganci? Shafin http://fha.gob.ng/ongoing-projects ya bada karin bayani.
Tsarin Koyarwa da Horarwa ta NDDC: Wannan tsarin yana ba da horo da tallafi ga matasa da suka kammala karatun digiri a yankin Neja Delta, tare da habaka kwarewa a aiki. Ya yi daidai da sashe na 17, manufofin zamantakewa na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya wanda ya nuna sadaukar da kai da adalci na zamantakewa, inganta yanayin rayuwa ga ‘yan kasa da dai sauransu. To amma, shin shirin yana fuskantar tsoma bakin ‘yan siyasa da cin hanci da rashawa? A ziyarci shafin https://nyis.nddc.gob.ng domin Karin bayani.
Tallafin kudi da lamuni ga kanana ‘yan Kasuwa: Shirin Tallafawan (wato Nano-Business Support) yana karkashin kulawar ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta tarayya, ya kasu kashi biyu, yana bayar da tallafin kudi ga kananan ‘yan kasuwa ta hanyar ba su naira dubu hamsin kowanne, yayin da a daya bangaren kuma akwai lamuni wanda ake ba ‘yan kasuwa. Manufar ita ce a taimaka musu su ci gaba da ba da gudummawa ga tattalin arziki. Wannan ya yi daidai da manufar sashe na 16 na kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda ya jaddada daidaiton rabon dukiya da albarkatu a tsakanin ‘yan kasa.
Babban kalubale a nan shi ne cewa zababbun wakilanku dole ne su sani kuma su shigarda sunaye a cikin jerin wadanda za su amfana tun tashin farko. Lalle wannan tsarin abun tunani ne!
A ziyarci shafin https://fedgrantandloan.gob.ng domin fahintar kofar ragon da aka shirya a tsarin.
Hakikanin Gaskiyar Al’amuran Nijeriya
Wannan ababen su ne abin da muke gani na faruwa ga shirye-shiryen guda 11:
Matsalolin Kudi – Duk wadannan shirye-shiryen suna bukatar kudi masu yawa. Rashin kudi da kuma tekun bashin da Nijeriya ke ciki babban kalubale ne ga aiwatar da shirye-shiryen.
Cin hanci da rashawa da almundahana -Wannan babban kalubale ne a Nijeriya. Batun almubazzaranci da kudaden gwamnati da rashin gaskiya su ne al’amuran da ake fuskanta yau da kullum.
Rashin Fadakarwa da Wayar da Kai -Shin akwai yuwuwar wadannan shirye-shiryen za su kai ga wadanda za su ci gajiyar shirin saboda rashin isassun kafen wayar da kan jama’a ko wahalhalun da ake samu wajen kaiwa ga wurare masu nisa? Fatan wannan rahoton shine taimakawa wajen yada wadannan shirye-shiryen daban-daban don isa ga wadanda zasu ci gajiyar shirin.
Karancin ababen more rayuwa – Rashin isassun kayayyakin more rayuwa kamar samar da wutar lantarki, sufuri, da sadarwa na iya shafar isar da shirye-shiryen da sa ido. Tuni matsalar kawar da tallafin wutar lantarki na shafar nasarar tsare-tsaren.
Kwarewar masu gudanar da shirye-shiryen na da alamun tambaya kuma kalubale ne.
Yiwuwar Dorewa da Tasirin Tsare-tsaren na Tsawon Lokaci – Masu gudanar da shirin suna bukatar nuna tasirin shirin na dogon lokaci da dorewa fiye da aiwatarwa da shirin a matakin farko ba hayaniya ba maras amfani.
Hadin kai Tsakanin Masu Ruwa da Tsaki – Shin akwai hadin gwiwa mai inganci tsakanin hukumomin gwamnati, kungiyoyin sa-kai, da abokan hulda masu zaman kansu?
Tattara bayanai da Kulawa – Samar da ingantattun hanyoyin tattara bayanai da hanyoyin sa ido suna da mahimmanci don tantance tasirin shirin da yanke shawara mai inganci.
Burinmu
Jama’a ka da su yi shakkar yin amfani da wadannan damammaki. Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba da tabbacin samar da ginshikin doka ga duk ‘yan kasa don cin gajiyar wadannan shirye-shirye.
Idan akwai batutuwan da suka shafi biyan bashin, Sashe na 42 na kundin tsarin mulki na iya zama kariya ta hanyar tabbatar da cewa babu wani dan kasa da ake nuna masa wariya bisa rashin ka’ida a cikin gudanarwa ko aiwatar da hanyoyin biyan basussukan.
A karshe, a matsayinmu na ’yan Nijeriya, bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba na dagewa a kan tabbatar da aiwatar da aikin gwamnati cikin gaskiya da rikon amana.
Tsari da adalci da ta fi dacewa ga duk ’yan Nijeriya abu ne mai yiwuwa nan gaba ba da jimawa ba!