Gwamnatin Jihar Bauchi ta ware Kashi 15.04 na gaba dayan kasafin kudin shekara 2025 ga bangaren ilimi. Kwamishinan kasafin kudi da tsaralamarin tattalin arziki, Aminu Hammayo, shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake hira da ‘yan jaridu a Bauchi.
Ya ce banagaren ilimi zai samu Naira bilyan 39.133 ma’aikatar ilimi mai zurfi zata samu Naira bilyan30.8.
- Gwamnatin Bauchi Ta Kaddamar Da Kwamitin Adana Kayan Abinci
- Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Fiye Da Biliyan 465 A Matsayin Kasafin Kuɗin 2025
Hammayo ya bayyana cewa ganin yadda bangaren ilimi ya samu kaso mai tsoka hakan na daga cikin kokarin da gwamnatin take yi, na kara bada muhimmanci ga lamarin daya shafi ilimi, saboda bunkasa Jihar.
Kwamishinan ya kara bayanin ya ce zuba kudin da aka yi na jari a bangaren ilimi, ana sa ran yin hakan zai taimaka wajen bunkasa ci gaban al’ummar Jihar.
Hakanan ma sashen lafiya an ware mashi Naira bilyan 70.228, wanda hakan shine kashi 15.08 na gaba dayan kasafin kudin.
Kwamishinan ya kara jaddada cewa yawan kudaden da ake kashewa wajen ayyuka sun karu a kasafi kudi na shekarar 2025 saboda a samu yadda za ‘a tafiyar da lamarin sabon albashi na Naira70,000 mafi karancin albashi,da kuma fanshon da ake tafiyar da shi ta hadin gwiwa,da kuma lamarin da ya shafi harkar fansh.Karin shi yasa aka samun kashi 25 saboda karin abinda ya shafi albashi.
Hammayo kara bayan ikan dalilan da suka sa kasafin kudin ya karu wanda ya hada da samun isassun kudaden da za’ayi ayyuka da kuma habaka jin dadin al’ummar Bauchi.
Jaridar LEADERSHIP Lahadi ta bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2025 wanda ya kai Naira bilyan 465.85 ga majalisar Jihar domin ta amince da shi ya zama doka.
Ya kunshi kudaden aiki da suka kai Naira bilyan 182.743 da kuma yadda za’ a tafiyar da ayyukan yau da kullum da suka kai Naira bilyan 113.248.