Hukumar Kula Da Ma’aikata ta jihar Bauchi ta sake korar wasu ma’aikatan gwamnati biyu masu suna Nasiru Samaila da Anas Jibrin bisa samunsu da laifin amfani da takardun bogi domin cinye ma wani mamacin kudadensa.
Ma’aikatan biyu, su na aiki ne a karkashin ma’aikatar kudi ta jihar an zargesu da karkatarwa da sama da fadi da naira N332, 000 mallakin wani tsohon ma’aikatacin ma’aikatar Jibrin Adamu Zalanga (wanda ya rasu ma a halin yanzu) wanda a cewar hukumar, wannan dabi’ar ta saba wa sashin dokokin aikin gwamnati sashi na 327.
- Wakilin Jaridar Leadership Na Kano Ya Rasu
- Kalubalen Hada Kan ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Da Ke Gaban Ganduje
Hukumar ta cimma wannan matsalar korar nasu ne a yayin zamanta karo na 18 da ya gudana a ranar 15 ga watan Agustan 2023.
A sanarwar manema labarai da jami’in yada labarai na hukumar Saleh Umar ya fitar a ranar Juma’a ya ce, “A yayin zaman da hukumar ta yi kan kes din kwamitin kula da ladabtarwa, ma’aikata guda biyu wanda aka samu da laifin amfani da takardun jabu domin samun damar karkatar da kudi da yawansu ya kai N332,000 mallakin wani tsoho kuma marigayin ma’aikacin ma’aikatar kudi na jihar Bauchi (Jibrin Adamu Zalanga)”.
“Wannan matakin nasu ya saba wa sashi 327 na dokokin tsarin aikin gwamnati kuma jami’an biyu sun amsa laifukansu a yayin amsa tambayoyin da ma’aikatar ta musu,” Umar ya shaida.
Malam Saleh Umar ya yi kuma yi bayanin cewa tun da farko ‘yansanda sun kama ma’aikatan biyu tare da gurfanar da su a gaban babban kotun majistire domin samun hukunci daidai da laifukansu.
A cewarsa a yayin zaman hukumar ta kuma amince da karin girma ga wasu jami’ai 73 bisa kwazonsu da cancantarsu, kana an yi sauyi ga wasu mutum 11.
Shugaban hukumar, Alhaji Abubakar Usman Madakin Bunun Bauchi wanda ya jagoranci zaman, ya ce, kesa-kesan badakar kudade da suke samu na matukar damunsu.
Ya gargadi ma’aikata da suke jin tsoron Allah a dukkanin ayyukansu inda ya ce duk wanda ya kuma ki ji to ba zai ki gani ba.
A fadinsa za su kara sanya ido wajen dakile irin wannan mummunar dabi’ar.
Idan za ku tuna dai a kwanakin baya hukumar ta dakatar da izinin daukan aikin Ibrahim Garba wanda ma’aikaci ne a hukumar kula da fansho ta jihar bisa kamasa da laifin cinye kudin wani mamacin dan fansho.