Daga Balarabe Abdullahi, Zariya
Kimanin kwanaki kenan da janye yajin aiki da Malaman jami’o’in Nijeriya suka yi. Wakilinmu ya sami damar zagaya sassan cibiyar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma sashin Jami’ar da ke Kongo, inda ya tarar da babu dalibai a harabobin Jami’ar.
Lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin masu wukar yankar magana na Jami’ar, hakarsa ba ta kai ga cimma ruwa ba, domin bai sami nasarar yin hakan ba, saboda wasu dalilai da suka hada da matakan ganin wadanda ya dace su ce wani abu kan yajin aikin ya yi tsauri ga wakilin namu.
Wani babban Malami da ke koyarwa a cibiyar Jami’ar ta Ahmadu Bello, wanda kuma ya nemi da wakilinmu ya sakaya sunansa ya ce, ba hakkin kungiyar Malamai ba ne su umurci dalibai su dawo harabar Jami’ar domin ci gaba daukar darussa, wannan hakkin mahukuntan Jami’ar ne.
Wakilinmu ya gano cewar, wasu kungiyoyin da suke Jami’ar, da suka hada da na manyan ma’aikata da kungiyar masu gudanar wasu ayyuka na musamman da dai wasu kungiyoyi na ci gaba da yajin aiki, a bisa wasu bukatu da suke neman gwamnatin tarayya ta biya masu shekaru da dama da suka gabata.
Wakilinmu ya gano cewar, ko da Malaman sun janye yajin aiki, mahukuntan Jami’ar babu yadda za a yi su kira dalibai daga gidajen iyayensu, domin kungiyoyin da aka ambata suna da matukar muhimmanci, domina babu yadda za a yi Malaman su gabatar da ayyukansu, ba tare da su ba.
Ammawasu labarai masu tushe sun ce wadannan kungiyoyi, sun sami matsaya a tsakaninsu da gwamnatin tarayya, wanda in sun amince da matsayar, akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba mahukuntan Jami’ar za su kada gugen dawowar daliban domin su ci gaba daukar darussasu.
Har ila yau wakilinmu ya gano cewar a duk lokacin da daliban suka koma harabar Jami’ar, ba za a dauki lokaci mai tsawo ba za su fara jarabawa a daukacin cibiyoyi da kuma tsangayoyin da suke Jamai’ar a Samaru da kuma Kongo.
Wani dalibi da ke nazarin aikin jarida ya shaida wa wakilinmu cewar, wannan yajin aiki da Malaman da kuma sauran kungiyoyin ma’aikatan Jami’ar ke yi ya kawo masu babbar cikas ga karatun da suke yi, musamman da zarar sun dawo, ba za su dauki dogon lokaci ba za su fara jarabawa.