A yau Juma’a ne aka gudanar da bikin bayar da kyaututtuka na Globe Soccer Awards na shekarar 2024, inda tauraron Real Madrid, Vinícius Jr, ya samu kyautar gwarzon ɗan wasa a ɓangaren maza.
Har ila yau, ɗan wasan na Brazil ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gaba, abin da ya nuna cewa zai kammala shekarar 2024 cikin wani yanayi mai ban sha’awa.
- Hukumar KNARDA Ta Horar Da Manoman Wake Tare Da Ba Su Kayan Aiki A Jihar Kano
- Zargin China Da Bautar Da Leburori a Gonar Tumatir a Xinjiang: Mene Ne Gaskiyar Lamarin?
Shi ma fitaccen ɗan wasan Real Madrid, Jude Bellingham, ya samu kyaututtuka guda biyu: kyautar mafi kyawun ɗan wasan tsakiya da kuma lambar yabo ta Maradona, abin da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a cikin manyan ‘yan wasan ƙwallon ƙafa na duniya.
Haka nan, an karrama Neymar Jr da wata lambar yabo saboda gudunmawar da yake bayarwa a harkar ƙwallon ƙafa a duniya.
Shi ma matashin ɗan wasa Lamine Yamal, ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa mai tasowa a bikin.