Biyo bayan harin ƙunar baƙin waken da aka kai a garin Gwoza na jihar Borno, yanzu haka an kama wasu mata biyu da ake zargin ‘yan ƙunar baƙin wake ne. Wani jami’in ƙaramar hukumar ya tabbatar da nasarar kama su, inda ya bayyana cewa an turo Mata ƴan ƙunar baƙin wake kimanin 30 zuwa Gwoza da nufin tayar da bama-bamai a wurare daban-daban. Ya zuwa yanzu huɗu daga cikin waɗannan ƴan ƙunar baƙin waken sun tayar da nasu Bam ɗin.
Daya daga cikin waɗanda ake zargin, wacce ta fito daga mashigar Pulka, ta tayar da Bam ɗin ne a lokacin da sojoji ke yi mata tambayoyi a wani shingen binciken ababan hawa, inda ta kashe kanta, da Soja ɗaya, da kuma ‘yar Civilian Joint Task Force (JTF). Sauran matan sun shigo Gwoza ne daga wurare daban-daban, ciki har da Pulka da tsaunin Mandara.
- Gwamnatin Kano Ta Musanta Bullar Cutar Kwalara A Jihar
- Ƴan Ta’addan Da Suka Kai Hari Borno Zasu Yabawa Aya Zaƙinta – Tinubu
A baya dai Darakta Janar na Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Borno (BOSEMA) Dakta Barkindo Saidu ya nuna damuwarsa kan kasancewar wata ‘yar ƙunar baƙin wake a yankin Pulka sakamakon hare-haren da aka kai a Gwoza.
Wannan kame dai zai kasance wata gagarumar ci gaba ne a yunƙurin da ake na daƙile ayyukan ta’addanci a yankin.