Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya sake nada Barista Ibrahim Muhammud Kashim, a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi, nadin kuma zai fara aiki nan take.
Idan za ku iya tunawa dai Ibrahim ya zama dan takarar gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani da aka gudanar daga bisani kuma ya janye bayan Bala Kaura ya fadi zaben fitar da gwani na shugaban Kasa.
- Da Diminsa: PDP Za Ta Sake Sabon Zaben Fidda Gwani Na Gwamnan Bauchi
- 2023: Duk Sanatocin Bauchi Masu Ci Babu Mai Komawa Sun Sha Kaye A Mazabunsu
A wata sanarwar da Kakakin gwamnan Jihar Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar a ranar Alhamis, ya shaida cewar nadin zai fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba.
A cewarsa, sake nadin Kashim din ya biyo bayan kwazo da kokarin da ya nuna, kyakkyawar tarihi, ladabi da biyayya, himma da kwarewa wajen sauke nauyin da ke kansa a dukkanin ayyukan da aka dora masa.
“Barr. Ibrahim Mohammed Kashim shi ne tsohon sakataren Gwamnatin jihar Bauchi. Gwamnan ya sake dawo da shi wannan kujerar ne bisa kokari da kwazon da ya nuna.” Cewar gwamnatin Bauchi.