Bayar Da Kula Wa Ga Kowanne Bangare Zai Kawo Karshen Rikicin Makiyaya Da Manoma –Danfulani

heardsmen

Daga Wakilinmu

Wani dan kasuwa da ke zaune a Zariya,  Alhaji Ya’u adamu Danfulani ya bayyana cewa, rikicin makiyaya da manoma na bukatar kulawa ta musamman daga bangaren gwamnati,  domin kuwa yin haka shi zai kawo karshensa.

Danfulanin ya sanar da haka ne cikin zantawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke kan titin zuwa Defot din sojoji da ke  Zariya a makon da ya gabata.

Danfulani wanda ya kasance fitaccen dan kasuwa a harkar takin zamani, kuma mai fada a ji a harkar noma, ya ce samarwa  da makiyaya matsuguni na dundundun, na daya daga cikin hanyoyin da za su kawo karshen rikicin makiyaya da manoma wanda  ya ki ci ya ki cinyewa a kasar na.

A matsayinsa na shugaban kamfanin Hulhulde Intanashonal, ya shawarci gwamnati da ta ba kowanne bangare kulawa ta musamman, da samar da matsuguni ga makiyaya tare da ba da ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu  don  kawo karshen rikicin.

Haka kuma kara da cewa, karanci abincin dabbobi ya sa Fulani makiyaya ke tafiye- tafiye  zuwa wurare don samarwa dabbobinsu abinci.

A cewarsa,”noma da kiwo tamkar Hassan  da Hussaini ne, dukkansu sana’a ce  wadda ke da asali, manomi bai iya rayuwa sai da makiyayi “.

Ya kara da cewa, kasashen da suka ci gaba kamar kasar Indiya sun samarwa da makiyaya matsuguni na musamma tare da samar musu da kayan more rayuwa kamar, makarantu don koyar da ‘ya’yan makiyaya da Asibiti da sauransu.

Ya ce hakan ya sa makiyaya  na gudanar da sanaar kiwo ba tare da shiga gonakin manoma don kiwo ba.

A cewarsa a wadannan kasashen, duk makiyayi za ka ga cewa manomi ne don ya rungumi  sana’ar kiwo da gudanar da  noma a wuri daya.

Ya ce yin hakan shi ne zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a kasar nan

Saboda haka sai ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta samar da takin zamani cikin lokaci don bunkasa noma da ciyar da kasa gaba a damuna mai zuwa.

Ya ce hakan shi ne zai ba su kwarin gwiwa da za su tunkari harkar noma cikin sauki ta yadda za su bada gudummwa don ciyar da kasa da abinci da samar da aikin yi

Sannan sai ya koka kan yadda gwamnati  ta ba wasu /yan kasuwa damar shigo da masara  cikin kasar nan.

Ya ce wannan zai iya durkusar da harkar noman  masara ta yadda zai rage musu karsashi da jajircewar da suka yi a baya wajen inganta noman  masara a Nijeriya.

Saboda haka sai ya yi kira  ga gwamnati da ta dakatar da wannan shiri na shigo da masara, da sauran kayan amfanin gona cikin kasar na, hakan shi ne zai ba manoma kwarin gwiwa don habaka noma tare da ciyar da kasa da abinci.

Exit mobile version