Connect with us

Hannunka Mai Sanda

Bazuwar Koronabairus A Nahiyar Turai

Published

on

Ga mai bibiyar wannan dan rubutu tun farko, ya kwana da sanin cewa, muna dauko abubuwa daki-daki ne bakin-gwargwado. Ke nan, ba abin mamaki ba ne mai karatu zai ga anjima da wuce waje, mu kuma sai yanzu ne muke yin tsokaci a kai.
A hankali a hankali ba tare da daukar lokaci ba, za mu gangaro batun wannan mugunyar cuta, tun daga sasannin Duniya da muke magana a kai, har mu iso wannan gari namu na haihuwa, Kano. Idan ka dauke Makka da Madina, da yawanmu, gari na uku da suke shauki da tsantsar kauna, ba zai wuce jihar Kano ba.
Gabanin tafiya zuwa ga gabatar da irin yadda wannan cuta ta Koronabairus ko COVID-19 ta fara ragargazar Nahiyar Turai, zai yi kyau fa mai karatu ya sani cewa, yanzu haka a Duniya, ba a fadar cikakken adadin wadanda ke kamuwa da wannan cuta ko suke mutuwa.

Hasashen Masana Game Da Yadda A Ke Kwangen Adadin Mutanen Da Annoba Ke Mamaya
Da farko masanan sun ce, da yawan lokuta, a na samar da adadin wadanda wannan cuta ta COVID-19 ta afkawa ne, ta fuskoki akalla biyu : i-adadin mutanen da cutar ta shafa suka warke, sai kuma, ii-wadanda suka rasu a sakamakon cutar.
A Duniyar yau, a kan gaza gane hakikanin adadin mutanen da wannan cuta ke tattare da su, saboda dalilai biyu. Na farko, wasu masu dauke da cutar, alamominta ba safai ne ke bayyana a gare su ba. Na biyu, da yawan Kasashen Duniya a yau, ba sa yin gwaji ga mutanen da a zahirance lafiyarsu kalau, domin gano, shin, suna dauke ne da shegiyar “COVID-19” koko a’a?.
Dalili na rashin tabbas game da ainahin adadin masu dauke da cutar na gaskiya a fadin Duniya, shi ne babban dalilin da ya sanya takwarori masu bincike, suka fi mayar da hankali kacokan, a kan adadin wadanda suka mutu a sakamakon cutar, sama da hakikanin adadin wadanda ke dauke da cutar. Babu shakka, wannan mayar da hankali kacokan bisa sanin adadin wadanda suka rasu, zai taimaka ne wajen gaza gane sauran ta’annati da cutar ke yi, yanzu haka a daukacin sasannin Duniya bakidaya.

A fili yake a Duniya cewa, wadanda suka rasu a sakamakon cutar ta COVID-19, alhali ba a yi musu gwajin cutar ba, kowa ya sani cewa, ba za a fadawa Duniya alkalamansu ba, cewa suna daga wadanda cutar ta aike zuwa lahira!
Da akwai wadanda su ka rika mutuwa da cutar Koronabairus hatta a nahiyar ta Turai, cikin wasu asibitocin da ba su da izinin duba masu dauke da sabuwar cutar a farkon lamari. Saboda haka, wadanda suka rasu a irin wadannan lokuta sakamakon cutar, babu wata hujja da irin wadannan asibitoci ke da a hannu, da za su tabbatar da cewa, koronar ce, alhali itan ce!!!.

Batun samun kwange daga ainihin adadin wadanda ke haduwa da ajalinsu cikin wannan Duniya sakamakon wata annoba da ta bayyana, wani lamari ne da ya jima yana faruwa. Sai bayan fakuwa ko bacewar annobar kwata-kwata ne, sannan daga bisani ake zuwa da alkaluman da suka fi karkata zuwa ga gaskiyar zance, sabanin lokacin da ake tsaka da fuskantar annobar.

Yayinda kakkarfar guguwar Maria ta ratsa tsibirin Puerto Rico cikin Shekarar 2017, a lissafin da Kasar Amurka ta fitar shi ne, an samu asarar rayukan mutane sittin da hudu “64” ne kacal. Amma sai ya zamana cewa, bayan annobar, bincike ya tabbatar da mutuwar mutane kusan dari uku “300” ne da suka rasu sakamakon ratsawar annobar cikin tsibirin, wadanda da daman mutanen, sun rasu ne a irin asibitocin da ba su da ikon gabatar da binciken marasa lafiya game da annobar a lokacin.

Hatta cikin Watan Mac na Shekarar 2020 (March, 2020) da ya kasance Kasar Italy, ta kere daukacin Kasashen Turai tarin yawan wadanda ke dauke da koronar, kamar yadda wani ayari na bincike game da cutar ya fadi. Sai dai waccan tawaga ta masu binciken da ake kira da Euromomo, ta kalubalanci hanyar da Kasar ta Italy ta bi, wajen fitar da alkaluman, don kuwa akwai nakasu ko tauyewa a lissafin.

Wadancan masu bincike sun fadi cewa, kawai Kasar ta Italy, ta gama ayarin wasu birane ne wuriguda, tare da ba da lissafin masu dauke da cutar, maimakon a bi biranen daya bayan daya daki-daki, a fitar da ingantattun alkaluman.

Ga masu bibiyar abubuwa sau-da-kafa, zai ci-karo a kwanakin baya da wani korafi da Kasar Taiwan ke yi cewa, Majalisar Dinkin Duniya, ba ta sanar da al’uma irin bayanan da take gabatar mata game da sha’anin cutar ta Koronabairus.

Ka da mu kaucewa batun da muka faro tun daga fitowa ta 11, wato shigar cutar Koronabairus zuwa ga yankin Turai.

Ranar 21 ga Watan Janairu, na Shekarar 2020 ne ake hasashen cewa wannan cuta ta Koronabairus ta shiga Nahiyar Turai. Bayan Watanni biyu da wasu Satika da shigar cutar, sai gashi ta rika burunkasa tamkar wutar daji.

Cikin Watanni kasa da uku da shigar cutar cikin waccan nahiya ta Turai, an tabbatar da wadannan alkaluma kamar haka;

1- Mutane kimanin dubu dari takwas da hamsin da biyu, da dari takwas da casa’in da tara (852,899) cifcif, sun kamu da cutar ta Koronabairus.

2- Mutane dubu saba’in da uku (73,000) kuma, sun rigamu gidan gaskiya, wato sun rasu.

3- Mutane kimanin dubu dari biyu da goma, da dari daya da ashirin da bakwai (210,127), sun samu waraka daga cutar. Sannan,

4- Sai da cutar ta Koronabairus ta shiga cikin iyakokin Kasashen na Turai a wancan lokaci akalla guda hamsin da bakwai (57).

An tabbatar da cewa, ranar 17 ga Watan Mac na Shekarar 2020, cikin kowace Kasa a yankin Turai, an tabbatar da samun cutar ta COVID-19. A karshe, Kasar Montenegro ce cikin nahiyar ta Turai, wadda a karshe aka tabbatar da cewa mutum guda daya ne jal (1) ya kamu da cutar a cikin kusan tsakiyar Watan da ya gabata na Mac.

An wayigari ran 18 ga Watan Mac na wannan Shekara ta 2020, sama da mutane miliyan dari biyu da hamsin ne hukumomi suka tilasa su zuwa ga zaman-gida na sai baba ta gani (lockdown) a yankin nan Turai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: