Mataimakin Sufuritandan ‘yansanda ya harbe wata lauya ‘yar jihar Legas mai suna Bolanle Raheem a unguwar Ajah da ke jihar a ranar Kirsimati.
Dan sandan da ba a bayyana sunansa ba wanda ke aiki a ofishin ‘yansanda na Ajah da tawagarsa an ce sun yi kokarin hana Raheem da ‘yan uwanta wuce wa ne yayin da suke komawa gida daga hidimar coci a ranar Kirsimati.
Raheem, an rahoto cewa, an harbe ta ne lokacin da motar da take ciki ta yi kokarin juyawa a karkashin gadar Ajah.
An garzaya da wacce aka harba zuwa asibiti amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarta. Inji rahoton Vanguard