Majalisar Wakilan Tarayyar Nijeriya ta bukaci Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da ta tabbatar da sanya ido kan lamuran da su ka shafi direbobin ababen hawa a fadin kasar, musamman a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Majalisar ta ce, bukatar hakan ya zama dole ne, domin tabbatar da kiyaye lafiya da rayukan jama’a, ta na mai neman ma’aikatar da ta kababa takunkumi ga direbobin da su ka ki bin matakan da su ka dace.
Wannan matakin ya biyo bayan kudirin neman hakan ne da dan majalisar, Hon. Chinedu Martin Emeka daga jihar Imo (PDP), ya gabatar a kwaryar majalisar dokokin kasa jiya.
Hon. Emeka ya yi bayanin cewa, a ‘yan kwanakin nan a na samun masu shiga harkar sufuri ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ke kara haifar da matsaloli kan sha’anin sufuri.
Nan take majalisar ta amince da kudirin bayan samun gudunmawar goyon baya daga wasu daga cikin mambobin Majalisar Dokokin ta Wakilai.