Masu kiwo karkashin inuwar kungiyar Masu Kiwon Kaji ta kasa (PAN) sun roki Gwamnatin Tarayya da ta ceci masana’antar kiwon kaji ta Nijeriya daga rugujewar da take fuskanta wanda yanzu masana’antar ke fuskanta sakamakon tashin gwauron zabi na farashin abincin Kajin da kuma abubuwan da su ka saba amfani da shi ciyar da kaji.
Sun bayyana cewa, kayan abincin da su ke ciyar da Kajinsu kamar su waken soya, farashinsu ya tashi matuka matsakaicin mai kiwon, inda yanzu farashin kayan ya karu daga Naira 115,000 wanda aka sayar da kowace tan a watan Agusta zuwa Naira 215,000 a watan Nuwambar shekarar 2020, inda hakan ya kai kashi 86,95 a cikin dari a cikin watanni hudu.
Da take magana ta wata sanarwa da aka sanya wa hannu aka kuma rabarwa da ‘yan jarida a Abeokuta a ranar Litinin data gabata, Shugaban kungiyar Kaji na Nieriya (PAN), Blessing Alawode, reshen Jihar Ogun, ta lura cewa tare da hauhawar farashin kayan abinci ba kakkuatawa, musamman farashin na waken soya, farashin kwai, nusamman na kaza daya na iya kaiwa tsakanin Naira 5,000 zuwa Naira 10,000 a lokacin bikin Kirsimeti dana sabuwar ahekara.
Sanarwa wacce aka yiwa lakabi da, masana’antar kaji, Zuba jari na Tiriliyan Naira a Nijeriya na fuskantar durkushewa a cikin sauri ya yin da farashin masara, maken soya ya ke ci gaba da tashi sama.
Ya yin da su ke neman agajin gaggawa daga Gwamnatin Tarayya da hukumominta kamar Babban Bankin Nijeriya, Hukumar Kwastam ta Najeriya, da sauransu, sun dukufa wajen ganin sun samar da mafita ta hanyar Gwamnatin Tarayya.
Alawode ta kuma yi zargin cewa, cin hanci da rashawa da a tsakanin masu sayar da abincin da masu fataucin, wadanda ne ke haifar da karancin na wucin gadi ta hanyar tara kayayyakin da fitar da su ta haramtacciyar hanya zuwa kasashen makwabta.
Ta ce, “A cikin watan Agusta na shekarar 2020, an sayar da masara da soya a kan Naira 170,000 da kan Naira 115,000 a kowace tan, tare da farashin kasuwa na abincin, inda ‘yan kasuwa a kan matsakaicin farashin na Naira 3,300 a kowace buhu mai nauyin kilgiram 25, inda kuma farashin masara ya kasance kan Naira 170,000 a kowace tan a watan Satumba, soya ya tashi zuwa Naira 125,000.
“A watan Oktoba, ya yin da manoma su ka yi farin ciki da masara kan ko wanne tan daya ta kai Naira 152,000, inda kuma tan na waken soya ya sake tashi zuwa Naira 150,000.”
A cewarta, ya zuwa yau, masara tan ta kai Naira 145,000, inda waken soya ya kai Naira 215,000, wannan ya nuna karuwar kaso 86.95 a cikin dari a cikin watannin hudu.
Ta bayyana cewa, “Taron tattara bayanan sirri game da batutuwan da su ka shafi karin farashin masara da kuma waken soya ya nuna tarin masarar da waken soya da ‘yan kasuwa su ka yi, wanda hakan ke haifar da karancinsu.”
A cewarta, fitar da waken soya da wasu masu noman su ka yi, rashin girbi mai kyau saboda raahin ungantaccen iri, hakan ma ya shafi fannin, inda ta ce, don haka, muna kira ga Gwamnatin Tarayyar ta hanyar Ma’aikatar Aikin Gona da ta hanzarta yin aiki a kan dakatar da fitar da waken soya zuwa kasashen da Nijeriya take makwabta da su har sai an wadatar da cikin gida.
Shugabar ta ci gaba da cewa, muna amfani da wannan damar don yin kira ga masu sayar da abincin na kasuwanci don nuna wani matakin la’akari a cikin farashin su kasancewar rayuwar masu kiwon kaji na da nasaba da fannin aijin noma.