Ikirari: Kwanan nan aka yada wani hoto da aka nuna “shafin farko” ne na jaridar PUNCH a soshiyal midiya inda aka nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 5 da miliyan dari tara (N5.9bn) wajen horas da matasa guda 177 kan yadda ake gyaran wayar hannu.
Cikakken Labarin: A wannan “shafin farkon” da aka yada, an rubuta baro-baro cewa, “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kashe naira biliyan 5.9 wajen horas da matasa 177 kan gyaran wayar hannu,” labarin da ya jawo maganganu da suka mai yawan gaske daga ‘yan Nijeriya.
Wani mai amfani da Instagram ya yi tsokaci a kan zancen inda ya ce, “Don Allah ko akwai wanda zai ba ni ruwan sha kofi daya, Nijeriya ta kusa sanya ni in suma! Ban da dukkan rancen kudin da ake karbowa, in ba a ce dabbobi ba, beraye da kwari sai kuma a ce … wai har yanzu biliyan na da ziro guda tara ne? Akwai bukatar mu #sakekarbarnaija #tsaftacenaija #sakeginanaija.”
Wani kuma ya hau Tuwita ya yi tsokaci kamar haka: “Do Allah, ko akwai gwanayen lissafi a nan? Don Allah ku lissafa, ina so in ga nawa ne ake nufin APC ta kashe a kan wadannan matasan bogin su 177?
“Ya ku Matasa, kafin ku goyi bayan haukan nan da ake kira APC, ku tuna da wannan kanun labarin. In da an yi amfani da wannan kudin ta hanyar da ta dace, ai da mun samu matasa masu amfanarwa.”
Tabbaci: Jaridar PRNigeria ta lura da cewa wannan hoton ya na da tambarin ‘watermark’ “- 6mdh – photogrid” wanda ya sa ake ganin sa kamar tambarin jaridar PUNCH na gaske ne aka dauko daga masu amfani da soshiyal midiya daban-daban, saboda haka sai mu ka yi amfani da hikimar bincike ta ‘reberse image search’ a manhajar Google, a karshe sai sakamakon ya nuna mana cewa hoton wanda ya yi kama da na bangon gaba na mujalla babu inda ya fito a cikin shafukan zahiri na jaridar PUNCH da ke soshiyal midiya, kawai wasu masu amfani da shafukan zumunta ne su ka rika tura shi nan da can a Tuwita da Instagram.
Daga nan jaridar PRNigeria ta tuntubi sashen yada labarai na Ma’aikatar Harkokin Jinkai domin tabbatar da gaskiyar wannan magana, to amma sai wani jami’i da ya roki mu sakaya sunan sa ya bayyana lamarin da “Labarin bogi.”
Sai dai da PRNigeria ta gudanar da bincike kan wasu muhimman kalmomi a wurare daban-daban, ta gano cewa duk da yake hoton da aka yada karya ne, shi labarin ba karya ba ne amma kuma rahoto ne da ya fito watanni hudu da su ka gabata.
Gaskiya ne cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana a cikin Afrilu 2022 cewa ta ware kudi naira biliyan N5.9 domin horaswa da samar da kayan aiki da biyan alawus-alawus a kowane wata kan Rukunin C na shirin ‘N-Power’ a Jihar Kano, ba wai a kan matasa 177 kacal ba. Gwamnatin ta nanata cewa kimanin matasa 16,629 ne su ke amfana da shirin (karkashin Rukunin C) a jihar, ta kara da cewa a kiyasi har mutum 18,042 sun ci moriyar shirin a Rukunin A da na B na shirin.
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta ba da wannan bayanin ta hannun Mai Taimaka wa Shugaban Kasa na Musamman a Koyar da Sana’o’i, Dakta Nasir Mahmoud, lokacin da ya wakilce ta a wajen bikin yaye daliban shirin ‘N-Skills’, wanda wani sashe ne na ‘N-Power’, wanda aka yi a Kano, inda aka horas da matasa 177 kan gyaran waya.
Wannan bayanin ne jaridar PUNCH ta dauka ta lauya shi ta buga labarin da ya yaudari masu karatu, wanda tuni ta gyara labarin.
Kammalawa: Bisa ga shaidar da jaridar PRNigeria ta harhada, mun gano cewa ikirarin wai Gwamnatin Tarayya ta kashe naira biliyan 5.9 kan horas da matasa guda 177 su iya gyaran waya ba gaskiya ba ne. An fara buga rahoton a cikin jaridar PUNCH (shi ma ba a shafin farko ba) wanda tuni sun gyara shi tunda matasa 177 din da ake magana wani sashe ne kadai daga cikin jimillar matasa 16,629 da za a horas a Rukunin C na shirin ‘N-Power’ a Jihar Kano wadanda za su amfana da naira biliyan 5.9 da Gwamnatin Tarayya ta kasafta. Haka kuma, hoton da ake yadawa ba daga ita kan ta jaridar PUNCH ya fito ba, kawai wasu ne su ka kirkire shi domin su yaudari jama’a.