Kamar yadda bincike daga wasu likitoci mata, Dr Aisha Yusuf da Dr Na’ima ya tabbatar, Maniyi ruwa ne da ke fitowa daga gaban namiji a lokacin saduwa da matarsa ko kuma lokacin da jinsin mace da namiji ke tarayya da juna.
A lokutta da dama mutane musamman mata kan tambayi likitoci ko akwai hadari ga lafiyar mace idan tana hadiye maniyin mijinta a lokacin da suke saduwa?
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Sanar Da Matakan Martani Ga Ziyarar Da Pelosi Ta Kai Taiwan
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 95 Za Su Yi Zabe A 2023 —INEC
Kamar yadda aka ruwaito a Shafin Facebook na Arewa Beautiful, wata likita Ba’amurkiya, Dr Jen Anderson ta yi kokarin bayyana amfani da illar da ke tattare da hadiye maniyin namiji wanda aka wallafa a shafin kiwon lafiya na ‘Heathline’ da ke shafin intanet.Binciken ya gano wasu abubuwa kamar guda takawas game da shan maniyyin.
Na farko, Hadiye maniyin namiji ba ya cutar da kiwon lafiyar mace domin maniyi na dauke da sinadarin ‘Glucose, sodium, citrate, zinc, chloride, calcium, lactic acid, magnesium, potassium wanda ke taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace.
Sai dai bincike ya nuna cewa mace za ta fara ganin amfanin wadannan sinadarori a jikinta idan tana yawan shan maniyyin ne kawai.
Abu na biyu da binciken ya gano shi ne, Hadiye maniyyin na kare mace mai ciki daga kamuwa da cutar hawan jini. Bincike ya nuna cewa maniyyi na dauke da sinadarin ‘Endorphins, estrone, prolactin, odytocin, throtropin da serotonin wanda ke hana mace mai ciki kamuwa da hawan jini.
Na uku, Hadiye maniyyi na kawar da damuwa ko kuma yawan fushi ga mata da maza saboda wadannan sinadaran da yake dauke da su.
Abu na biyar da binciken ya gano shi ne, ana iya kamuwa da cututtuka na sanyi da ke kama al’auran mutum. Binciken ya nuna cewa mace za ta iya kamuwa da cututtuka irin na sanyi kamar su ‘Gonorrhea, Chlamydia, Syphilis da sauran su sannan kuma da kanjamau idan har namijin na dauke da wadannan cututtuka.
Sakamakon binciken na biyar shi ne, shan maniyyi yana kara kyan fatar mace musamman wajen hana kuraje a fuska.
Na shida, an gano cewa hadiye maniyi na sa barci mai nauyi. Hakan na yiwuwa ne a dalilin yadda maniyyin yake dauke da sinadarin ‘Melatonin’ wanda ke taimakawa wajen sa bacci mai nauyi.
Na bakwai, shan maniyyi yana kara kiba a jiki domin akwai kitse daban-daban har kashi biyar zuwa bakwai da ke sa kiba a jiki.
Abin da binciken ya gano na takwas shi ne, maniyyi kan dan yi wari, sai dai likitan ta Amurka ta bayana cewa warin maniyi ya danganta ne da irin abinci da tsaftan namiji. Wani yakan yi dandanon siga-siga, wani kuma gishiri-gishiri.