Connect with us

KASUWANCI

Bincike Ya Tabbatar Da Cewa Ana Cinikayyar Da Biliyan 100 Ta Yanar Gizo

Published

on

Dimbin cinikayyan da ake yi ta yanar gizo a halin yanzun ya karu da kimanin kashi 44 cikin 100 a shekarar da ta gabata a kasashen Ingila da Amurka da dala bilyan 52, kamar yanda wani bincike ya tabbatar da hakan. An kiyasta yawan cinikayyan a duniya ta yanar ta gizo yana gab da kai wa dala bilyan 100.

Kamar yanda ake sanya tallace-tallace ta hanyar dillalai, da yanda ake gudanar da kasuwancin ta yanar gizo inda ake yin cinikayyan kai tsaye a tsakanin masu saye da masu sayarwa ta shafuka makamantan su Amazon Aleda. Yanda kasuwancin ke habaka ya nu na bukatar yin wani abu kan yawan koken da ake samu daga mashahuran kamfanonin kulla kasuwancin na, Procter & Gamble da Unileber, kan yawaitan damfaran da ake yi ta hanyar yin cinikayyan a yanar ta gizo.

Hakanan batun tabbacin samun abin da ka gani ka kuma saya a yanar ta gizo a lokutan da aka tallata maka su yana kara karya gwiwar ‘yan kasuwan yana kuma karfafa masu neman hanyoyin da za su tabbatar da tsaron lafiyar abokanan cinikin na su, kamar yanda binciken na Damian Ryan ya nu na, wacce abokiyar aiki ce a kamfanin akantoci na kasar Ingila.

“Binciken namu ya gano wannan kasafin kudin yana zuwa ne daga abin da kafafen yada labarai ke kashewa, zai kuma iya yin tasiri da abin da cibiyoyin kafafen yada labaran suke yi,” ta kara da cewa, binciken na Moore Stephens, wanda aka yi shi ta hanyar tallatawa da tuntuba, WARC, ya shafe kamfanoni 800 da suke a arewacin Amurka, kasashen Asiya- Pacific da kuma kasashen Turai.

Binciken ya gano cewa, kayayyaki a kasar Ingila da arewacin Amurka suna kashe kashi 23 na kasafin kudin na su ne a kan tallace-tallacen, wanda hakan ya daran ma kashi 16 da suke kashewa a shekarar da ta gabata. Hakanan kashi 63 na ababen kimiyya a arewacin Amurka, ne suke kashewa in an kwatanta da kashi 44 da suke kashewa a shekarar da ta gabata.

Hakanan akwai damuwa kan bayanan da mabubbugar bayanai ta Google da Facebook kan bayanan da suke Tarawa. Wadannan su ne manyan shafukan tallace-tallacen na yanar gizo. Dokokin su sun sanya da yawan masu yin tallace-tallacen a yanar gizo ko dai su narke a cikin su ko kuma su durkushe baki daya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: