Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, karkashin jagorancin Mai shari’a Simon Amobeda, ta umarci alkalai Farouk Lawan Adamu da Zuwaira Yusuf su yi murabus cikin sa’o’i 48 daga matsayinsu na shugabannin kwamitocin shari’a biyu.
Wannan hukuncin ya kasance wani bangare ne na ƙarar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya shigar, wanda ya nemi dakatar da binciken da gwamnati mai ci ke yi a kansa.
- Xi Jinping Ya Gana Da Vladimir Putin
- Masu Garkuwa Sun Kashe Ɗan Alƙaliya, Sun Nemi Miliyan 300 Kafin Sako Ragowar Ƴaƴan
Mai shari’a Amobeda ya bayyana cewa alkalan ba za su iya zama alkalan manyan kotuna da shugabannin kwamitocin ba, ya yi gargadin cewa rashin yin murabus zai haifar da rasa mukamansu.
Kotun ta soki gwamnan da nada alkalan ba tare da vai wa hukumar EFCC ko ICPC damar gudanar da bincike a kan Ganduje ba.
Alkalin ya jaddada cewa matakin da gwamnan ya dauka, ya saba wa raba madafun iko tare da yin Katsa-landan ga bangaren shari’a.
Ya ba da umarnin cewa alkalai Adamu da Yusuf su gaggauta yin murabus daga mukamansu tare da daina gudanar da ayyukan zartarwa na harkar shari’a.