Gwamnatin Birtaniya ta bayyana damuwarta tare da yin Allah-wadai da kisan fursunoni 33 da ’yan bindiga suka kashe a jihar Zamfara, duk da cewa an biya su kuɗin fansa Naira miliyan 50 kafin kisan.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigar da suka kai harin ƙarƙashin jagorancin shahararren ɗan ta’adda mai suna Ɗan Sadiya, sun sace fiye da mutane 50 a garin Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda, kafin daga bisani su saki mutum 17 daga cikinsu, yawancinsu mata, bayan karɓar kuɗin fansar.
- Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
A wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata dangane da shirin faɗaɗa aikin cibiyar haɗin gwuiwa ta yaƙi da garkuwa da mutane, mai wakiltar Birtaniya a Nijeriya, Gill Levers, ta bayyana cewa satar mutane da garkuwa da su babban laifi ne wanda ke dagula zamantakewa da ci gaban al’umma. Ta ƙara da cewa hakan yana shafar lafiyar ƙwaƙwalwa da jiki na mutane, kuma dole ne a kawo ƙarshensa.
Levers ta bayyana cewa an ƙirƙiro Cibiyar Yaƙi da Garkuwa da Mutane a matsayin wani shiri na shekaru uku domin haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro na Nijeriya wajen yaƙi da garkuwa da mutane. Cibiyar za ta riƙa tattarawa da nazari da raba daftarin bayanai ga ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.
Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Kasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka, ya ce cibiyar tana aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunonin Soji da jami’an tsaro tun kafuwarta, inda take taimakawa wajen daƙile hare-haren garkuwa da mutane a faɗin ƙasar. Ya ce cibiyar na ci gaba da gina dangantaka da hukumomin tsaro a matakin jihohi domin samun sakamako mai kyau a matakin ƙasa da na ƙasa-ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp