Shugaban kungiyar ‘yan fansho ta kasa (NUP), Godwill Abomisi da shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kano, Kwamred Kabiru Inuwa sun bayyana cewa ware kudi har sau hudu da hukumar fansho ta Jihar Kano, karkashin shugabancin Alhaji Muhammad Fagge ta yi don biyan tsofoffin ma’aikata da suka bar aiki ko kuma wadanda suka kwanta dama abun a yi ko yi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ne.
Sun ce gwamnan ya nuna tausayi da kashi ‘yan fanshon Kano da ma sauran al’ummar Kano baki daya.
Sun dai bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da naira biliyan 6 don biyan ‘yan fasho hakkinsu a karo na hudu da Gwamnan Kano, Abba ya yi rana Alhamis da ta gabata.
Haka kuma sun ce abu ne da yake karawa ma’aikayta karfin gwiwa na kyakywar makoma muddin aka samu gwamnoni irin Gwamna Abba, sannan sun gamsu da yadda ake biyan albashi kan lokaci da kuma biyan hakkokin tsofoffin ma’aikata.
Shugaban kungiyar NUP kasa reshen Jihar Kano na rikon kwarya, Kwamared Shuaibu Musa Jibrin ya ce wannan abun da Gwamnan Kano ya yi wa duk wani dan fansho a Kano na biyansa hakkinsa shi ne kyautatawa da kuma kara musu kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp