Boko Haram: Kwamandan NSCDC Ya Koma Borno Da Zama

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Kwamanda-janar na rundunar tsaron ,civil defence corps’ na kasa, Abdullai Gana, ya koma jihar Borno da zama, matakin wanda ya biyo bayan umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar na ya koma arewa maso-gabas da zama.

An bai wa Kwamanda-janar din umurnin ya tattare nasa-ya-nasa zuwa yankin tare da hada hannu da karfe da sojan Nijeriya da gwamnatocin Yobe da Borno da Adamawa, sannan ya tabbatar ya tura jami’an tsaron ‘jar-kwala’ domin bayar da tsaro ga makarantun da aka yanto yankunan su da ke cikin wadannan jihohin.

Haka zalika, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa daukar wannan matakin ya zama dole, ta duba ga yadda a cikin yan kwanakin nan lamurran tsaro ke tabarbarewar- ta hanyar kai sabbin hare-hare a makarantun yankin, kuma da yadda mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da daliban makarantar Dapchi a jihar Yobe.

Mista Gana ya samu gagarumar tarba daga kwamandan rundunar sojojin ‘Operation Lafiya Dole’, Manjo-janar Rogers Nicholas a babbar hedkwatar tsaro ta sojojin dake Maiduguri.

Exit mobile version