Boko Haram Sun Kona Kauyen Kirchinga A Adamawa

Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu, a harin sunkuru da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram suka kai a kauyen Kirchinga dake karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa; inda suka kona gidaje, suka washe shaguna.

Kauyen Kirchinga ya na da makobtaka da dajin sambisa, kuma kusan dukkan kauyen sun babbaka shi, kamar yadda wanda suka tsira da rayukansu suka shaidawa manema labarai.

Da misalin karfe 5 na yammacin jiya Talata ne tsagerun suka kai harin, shaidun gani da ido sun ce mayakan sun zo ne a kan babura da motocin akori-kura, inda a take suna zuwa suka fara bude wuta kan-mai-uwa-da-wabi.

Exit mobile version