Rahotanni daga kasar Chadi na cewa sojojin ƙasar sama da 40 suka rasu sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kai wani sansaninsu.
Wannan na cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Lahadi.
- Muna Fama Da Taɓarɓarewar Tattalin Arziƙi Da Wutar Lantarki – Gwamnonin Arewa Da Sarakuna
- Jami’an Kiwon Lafiya Na Mozambique Sun Koma Gida Bayan Halartar Horon Samun Kwarewa A Kasar Sin
Ta ce mayakan Boko Haram sun kai harin ne sansanin soji da ke tsibirin Barkaram a yankin tafkin Chadi da ke Kudu Maso Yammacin kasar, wanda ke da iyaka da Nijeriya.
Rahotanni sun ce da misalin karfe 10 na daren Lahadi mayakan suka kaddamar da farmakin, inda suka ci karfin sama da sojoji 200 da ke wannan sansanin.
Sanarwar ta tabbatar da mutuwar sojoji akalla 40, yayin da majiyoyin yankin suka ce adadin sojojin da suka mutu sun haura 60, tare da jikkata wasu da dama.
Majiyoyin sun ce, maharan sun mamaye sansanin har zuwa wayewar garin Litinin, inda suka yi awon gaba da makamai da alburusai masu tarin yawa, bayan sun kone sansanin sojin.
Shugaban kasar Janar Mahamat Idriss Deby, ya kai ziyara sansanin da safiyar ranar Litinin, inda ya kaddamar da rundunar Haskanite da za ta yi farautar maharan.