Boko Haram ta saki akalla ‘yan gudun hijira tara daga cikin sama da 200 da ta sace a Arewa Maso Gabas.
Shugaban Hukumar Bayar da Agaji (NEMA), Barkindo Saidu, ya ce an ga mutanen tara, wadanda duka mata ne da ‘yan mata, a sansanin ‘yan gudun hijira na Ngala a Jihar Borno.
- Wainar Da Aka Toya A Taron Majalisar Zartarwar Jihar Zamfara Na 18
- Tinubu Ya Umarci Jihohi Su Bai Wa Ma’aikata Kyautar Kudin Rage Radadi
“Ma’aikatan sansanin ‘yan gudun hijirar sun bayar rahoton cewa mutum tara sun koma. An gan su a sansanin ‘yn gudun hijirar,” kamar yadda Saidu ya shaida.
Sama da mata 200 da ‘yan mata da maza, wadanda suka bar sansanin gudun hijirarsu don neman itace a Ngala da ke Jihar Borno mayakan Boko Harama suka yi garkuwa da su.
Kungiyar yan ta’addan wacce ke da matsuguninta a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya ta yi karfi zuwa kasashen Chadi da Nijar da Arewacin Kamaru da kuma Mali.
Mayakan na Boko Haram na da alhakin kai hare-haren da suka yi sanadin tserewar dubban mutane daga matsugunansu da kuma salwantar rayuwa da dukiya mai tarin yawa.