Boko Haram A Yobe: ’Yan Sanda 235 Suka Rasu Cikin Shekaru 6 –Kwamishinan ‘Yan Sanda

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

A ranar talatar farkon wannan makon, rundunar yan-sandan Nijeriya a jihar Yobe ta tabbatar da cewa ta yi asarar manyan jami’an ta da ƙanana 235, ta dalilin tarzoma da auukan ƙungiyar Boko Haram a tsakanin shekaru shida da suka shuɗe.

Kwamisginan yan-sandan jihar Yobe, Mista Abdulmaliki Sumonu ne ya bayyana haka a sa’ilin da yake karɓar kyautar girmamawa daga ƙungiyoyin al’umma masu zaman kan su; masu kula da al’amurran yadda ayyukan tsaro ke gudana a jihar Yobe.

Abdulmalik ya ce wannan takardar girmamawar, kai tsaye yabo ce gare su tare da waɗanda suka rasa rayukan su wajen sadaukar da rayukan su a fagen ayyukan su ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya.

‘‘wannan takardar girmama, ba kawai ta kwamishinan yan-sanda bace, ta ɗaukwacin rundunar yan-sanda ce waɗanda suka sadaukar da rayukan su wajen kare martabar Nijeriya.” Inji shi.

Haka zalika kuma, ya ce wannan karramawa ce wadda zata ƙarawa yan-sandan karsashi tare da ƙara musu zimma a fagen aikin su. Ya ƙara da cewa ‘‘a irin wannan jagorancin ne yake ƙarfafa gwiwar kowanne ɗan-sanda a Nijeriya tare da kuzari a sha’anin ayyukan su wajen sadaukar wa.’’

Bugu da ƙari kuma, kwamishinan ya yaba da haɗin gwiwar da rundunar yan-sandan ke samu daga takwarorin ta na tsaro wajen cimma muradun al’ummar jihar na cikakken tsaro.

A hannu guda kuma, shugaban wannan tawagar, Mista Maurice Orwough, sun yaba da ƙoƙarin kwamishinan yan-sandan a jihar Yobe dangane da amfani da ƙwarewar sa a sha’anin tsaro a lokacin rikicin Boko Haram a jihar Yobe.

‘‘wannan karramawa ce ta girmamawa dangane da gagarumar gudumar da ya bayar kana kuma domin ƙarfafar gwiwa ga ayyukan su.” Ya ce.

 

Exit mobile version