Borno: PDP Ta Yi Tir Da Tsadar Kayan Masarufi Da Matsalar Tsaro A Karkashin APC

Borno PDP

Daga Khalid Idris Doya,

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Borno, ta nuna damuwarta matuka dangane da hauhawar farashin kayan masarufi gami da matsalolin tsaro tare da wasu ‘yan batutuwa da suke jibge a karkashin jam’iyyar APC.

PDP tana mai cewa tabbas jama’a suna fama da kuncin neman abun da za su kai bakin salati da kuma kalubalen tsaro da ya jima yana addabarsu wanda an gagara shawo kan su ne a sakamakon gazawar gwamnatin APC.

Shugaban jam’iyyar PDP a Borno, Usman Mahdi Badairi, shi ne ya shaida a jiya lokacin da suke ganawa da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi tare da mambobi da magoya bayanta a Maiduguri.

Badairi ya jinjina wa mambobin jam’iyyar PDP a bisa aikin hadaka da suke yi wajen kawo cigaban jam’iyyar a matakin jihar, sai ya horesu da su cigaba da hakan domin nasarar jam’iyyar a nan gaba.

Shugaban yana mai bada tabbacin cewa mambobin PDP ba za su yi zabin tumun dare na wadanda suke jagorantarsu a jam’iyyar ba.

Ya kuma nemi mambobin jam’iyyar da su kara hada kansu su ci gaba da zama ‘ya’yan tafiya daya domin kara samar wa jam’iyyar dumbin nasarorin da suka dace.

Daga bisani ya umarci shugabanin jam’iyyar na kananan hukumomi da mambobinsu da su koma kananan hukumominsu domin shirye-shiryen babban taron zaben jam’iyyar da ke tahowa.

“Mun damuwa matuka gaya bisa gazawar gwamnatin APC, ta fuskacin hauhawar farashin kayan abinci, hauhawar matsalar tsaro, rikicin tsarin jama’a, da kuma yawan ciwo bashin da gwamnati ke yi. Wadannan ababen matsaloli ne manya-manya.”

Shugaban ya bada tabbacin cewa dukkanin mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na PDP sun shaidi yadda daruruwan mambobin APC ke ficewa daga jam’iyyar zuwa PDP, don haka ne ya nemi su kara rungumar jam’iyyar dari bisa dari.

Exit mobile version