Daga Muhammad Maitela, Maidugur
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa ta kashe tsabar kudi har naira biliyan goma sha hudu (N14bn) wajen gina wasu muhimman hanyoyin mota guda 22; daga shekarar 2016 zuwa wannan shekara ta 2017.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin kwamishinan ayyuka, gidaje da sufurin jihar Borno wato Alhaji Adamu Lawan, a sa’ilin da yake ganawa da manema labarai a ofishin sa dake Maiduguri, babban birnin jihar.
Kwamishinan ya fara da bayyana cewa, a cikin shekarar da ta gabata(2016) gwamnatin jihar ta tsara kashe naira biliyan 56 domin gudanar da muhimman ayyuka 60, inda kuma ya kara da cewa sama da kaso 80 a cikin adadin ayyukan an hannun ta su ga sashen kula da ayyukan ma’aikatar.
“Yayin da ayyukan guda 26 daga cikin wannan adadi na 60 an riga an kammala su, alhalin kuma 13 daga cikin su aiki a kan su yana gudana, yayin da kuma 22 suna jiran amimcewa”. Inji shi.
Alhaji Lawan ya ce daga cikin wadanda aka kammala sun kunshi na Bulumkutu-Tsallake, Abbaganaram-Gongolong, da Magoram, Bulabulin hadi da wanda ke kan titin Lagas, a jihar.
Sauran kuma sune na rukunin gidajen Mala Kachalla-Ibrahim Taiwo da hanyar filin jirgi da titin Ndurimari. Sannan kuma ya ce wasu hanyoyin sun hada da gina gadoji tare magudanun ruwa.
Alhaji Adamu Lawan ya kara da bayyana cewa, gwamnatin jihar Borno ta tsara yadda shimfida hanyoyin yankunan karkara guda biyar wadanda matsalar tsaro ta jawo aka jingine aikin su. Hanyoyin karkarar sune ta Jere zuwa Mafa, Gamboru zuwa Wulgo ta shiga Ngala sannan da cikin garin Gamboru da Ngala.
Bugu da kari kuma, ya nunar da cewa” wasu daga cikin kaya da na’urorin da ma’aikatar ayyukan ta saya sun hsda da na’urar buga bulo motocin share hanya da masu loda kasa 12, motocin dakon kasa(tipper) 600 da masu markade siminti da dutsi da makamantan su, mallakar jihar”.
Har wala yau, kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayo motocin bas masu kujerun zama-32 guda 70 ga hukumar sufurin jihar ( Borno Edpress Transport Corporation) domin ta iya gudanar da ayyukan ta cikin tsanaki.