Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta ci gaba da zama ta daya a fagen kwallon kafa a duniya, bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta fitar da jadawalin kasashen ranar Alhamis din da ta gabata.
Bayan da Brazil ke mataki na daya, kasar Belgium ce ke biye da ita, sai Argentina ta uku, wadda ta maye gurbin Faransa mai rike da kofin duniya, sai Ingila ta ci gaba da zama a mataki na biyar, sai Sifaniya da ta koma ta shida ta hau kan Italiya, wadda ke rike da kofin nahiyar turai na Euro 2020, wadda ta koma ta bakwai.
Tawagar Netherlands ce ta takwas, sannan Portugal ta tara da kuma Denmark, wadda take cikin goman farko. Kasar Medico ta fita daga jerin goman farko, wadda take ta tara a baya, yanzu ta koma ta 12 tana biye da Jamus ta 11.
Jerin goman farko a tamaula a Afirka
Senegal, Morocco, Tunisia, Nigeria, Kamaru, Masar, Algeria, Mali, Cote d’Iboire, da kuma Burkina Faso.