Wata yarinya ‘yar shekara 15 da ake kira Yafalmata Alhaji Mustapha an kama ta a sansanin ‘yan gudun hijira na Charamari da ke Monguno, jihar Borno, bisa zargin ta jefa jaririn da ta haifa a bayan gida.
An kama Yafalmata bayan da mazaunan sansanin suka gano gawar jaririn da aka jefar da karfe 6 na safe a ranar Alhamis, wanda ya sa ‘yansanda suka fara bincike nan take.
- Fasaha Da Balagar Harshen Manzon Allah (SAW)
- Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 16 A Borno Bayan Sun Kawo Hari Barikinsu
Bisa ga majiyoyin tsaro, jami’an ‘yansanda da ma’aikatan kiwon lafiya sun isa wurin don gano hujjoji da kuma ɗaukar gawar jaririn zuwa Asibitin Janar na Monguno.
Wani likita ya tabbatar da mutuwar jaririn a lokacin da aka kawo shi asibiti, kuma an shirya binciken gawar don gano musabbabin mutuwar.
Daga bisani aka mika gawar ga shugaban sansanin domin a binne shi bisa ƙa’idojin Musulunci.
‘Yansanda sun ce ana ci gaba da bincike don gano cikakken bayani game da lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp