An yi babban wasan kwallon kafa na farko cikin shekaru 30 a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, wasan dai ya samu halartar dubban masu kallo ya kuma zama tarihi.
A karon farko cikin shekaru 30, dubban jama’a sun taru a filin wasan kwallo na birnin Mogadishu domin kallon wani wasan dare da aka yi a birnin, wanda ake kwatantawa a matsayin wanda yafi kowane hadari a duk fadin duniya.
Dubban masoya kwallon kafa ne suka taru a filin wasan Konis, wanda hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta gyara.
Koda yake wasan na karshe ne a wata gasar matasa masu shekaru 16 zuwa 18 da aka hada, amma ya kasance cikin tsauraran matakan tsaro, kuma abin tarihi ga birnin na Mogadishu, wanda ya ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.