Buhari A Shekaru 77: Gwarzon Yaki Da Rashawa

Barkan mu da sake haduwa a wannan filin namu mai albarka filin Hangen Nesa. A yau za mu dan ce wani abu kan rayuwar shugaban kasa Muhammad Buhari; idan za ku dai ina tunawa, Muhammadu Buhari yayi bikin karin shekara ne daga cikin shekarunsa a ranar 17 ga watan Disamban nan. A bisa haka ne za mu nazarci wasu daga cikin rayuwarsa musamman na gwagwarmaya da yaki da cin hanci da amsar sharawa.

A wannan makalar za mu yi kokarin kawo cikakken tarihin rayuwar shugaban kasa Buhari, amma kafin nan, za mu bibiyi yadda Buhari ya samu kansa a matsayin shugaban kasa a daidai gabar da Nijeriya take tsananin fuskantar cin hanci da amsar rashawa a bisa munanan dabi’un wasu marasa kishin kasa.

Nijeriya a jiya koma na ce har yanzu, ta samu kanta cikin manyan matsaloli na rashin aikin yi ga matasa, sata, fashi da makami, matsalar tsaro, durkushewar tattalin arziki, gami da sauran matsalolin da suka mamaye kasar; a gabar da Buhari ya amshi mulki da zimmar kawo sauyi da gyara; gyaran nan ba zai samu ba, dole ne sai an samu wadanda za su ji babu dadi, a bisa hakan ne kuwa suke hujumi da matakan da Buhari ke dauka na kawo sauyi da gyara a kasar nan.

A duk halin da ka ce za ka yi gyara, tilas fa, dole ne sai ka fuskanci tirjiya da matsaloli daga wadanda gyaran ta shafa kai tsaye; musamman idan muka dauko batun cin hanci da amsar rashawa wadanda suka mamaye ma’aikatu, makarantu, ofis-ofis kai za mu iyacewa koma ina, har kasuwanninmu rashawa bai bari ba. A gabar da kuma kowa ke neman jin dadi da walwalar rayuwa.

Buhari mai shekaru 77 ya amshi mulkin Nijeriya a gabar da rashawa da cin hanci suka samu gindin zama a wannan kasar tamu; to amma cikin shekaru hudu zuwa biyar, za mu iya yabawa da jinjina wa kokari da sa’ayin Muhammadu Buhari na sauyawa da daidaito da matsalolin da suka yi wa Nijeriya katutu.

Ko mutum bai son Buhari, ya shaidi cewar zuwa yanzu an samu raguwar cin hanci da amsar rashawa, kuma bugu da kari ma, za mu iya shaida cewar shugaban kasa Buhari bai da niyyar handame dukiyoyin kasar nan, illa iyaka neman kawo gyara da ci gaba wa kasar, duk da har zuwa yanzu wasu na kallon wasu matsaloli sun gaza daukar saiti, amma dai masu nazari za su iya hango cewar tabbas an samu gagarumar sauyi da ci gaba wajen dakile cin hanci da rashawa gami da dakile masu wannan dabi’ar cin karensu babu babbaka.

Buhari ya samar wa Nijeriya kima da mutunta a idon duniya ta fuskacin rage cin hanci da kwasar dukiyar kasa da wasu zababbun ke yi; abun takaici ne wasu su kwashi dukiyar kasa su kai wasu kasashen su boye, irin wanna halin ya ragu sosai a gwamnatin Buhari. Nijeriya za ta ci gajiyar yukurin Buhari kan dakile rashawa da cin hanci nan gaba, nan gaba ne jama’a za su fahimci rayuwa da gudunmawar da shugaba Buhari ya taka wurin hana cin hanci ci gaba.

Wani abun karin takaici kan matsalar cin hanci da rashawa shine; matsalolin da suke kasarmu da muka jero kadan daga ciki a sama, rashawa da cin hanci sune suka hana a shawo kansu, babu ta yadda za a yi a ciyar da kasar nan gaba, ba tare da takewa cin hanci burki ba.

A yau a Nijeriya za mu iya cewa da badin taimakon da Allah ya mana da zuwan Buhari a irin wannan gabar ba, da za mu iya cewa Nijeriya sai dai mu dauki hannu mu daura a kaaa domin wasu marasa kishin kasar sun gama wawushe mana dukiyar kasa; Alhamadullah, yanzu tattalin arzikin Nijeriya na ta farfadowa a sakamakon jajircewar Buhari mai shekaru 77 a duniya.

Yabon gwani ya zama dole, a daidai lokacin da Buhari ke bikin shekaru 77 a duniya, ya dace mu karramashi da lambar gwarzon yaki da rashawa da cin hanci a Nijeriya. Bar n ace wani abu kafin masu na dire, ban ce babu matsaloli a gwamnatin Buhari ba, shi ya sa ma a shekarun nasa na dauko ababe guda biyu na jinjina masa a kai, yaki da rashawa da cin hanci. Allah taimaki Nijeriya da masu kishinta.

Waye Muhammadu Buhari?

Muhammadu Buhari dai an haifeshi ne a ranar 17 ga watan Disamban shekarar 1942 a garin Daura ta jihar Katsina.

Ya kasance shugaban Nijeriya a zamanin mulkin soja da kuma shugaba a zamanin farar hula. Ya shugabanci Nijeriya a zamanin mulki soji a shekarar 1984 zuwa shekarar 85, sannan aka zabeshi a matsayin zababben shugaban kasa a shekarar 2015, aka sake zabinsa a zango na biyu a shekarar 2019; yanzu haka shine shugaban Nijeriya mai cikakken iko.

An haifi Buhari ne a cikin tsatson Fulani. Babansa shine Hardo Adamu (Shugaban Fulani). Hardo Adamu yana da ‘ya’ya da yawa, Buhari shine dansa na 23.

Mahaifiyar Buhari ita ce, Zulaihat, ta haifi danta da kanta daga bisani mahaifinBuhari, ya rigamu gidan gaskiya, (Hakan ya faru ne a lokacin da Buhari ya kai shekaru hudu a duniya).

Buhari ya samu ilimi daidai gwargwado a jihar Katsina, daga bisani ya shiga horon soji a jihar Kaduna, sannan ya samu ilimi a Birtaniya da kuma kasar Amurka.

Yana da hannu a juyin mulkin da aka yi wa Yakubun Gowon lokacin da aka hambarar da mulkinsa a shekarar 1975, kuma aka nadi shi gwamnan jihar arewa maso gabas (Yanzu ita ce jihar Borno) wanda ya yi na tsawon shekara guda.

A zamanin mulkin shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo, ya nada Buhari kwamishinan tarayya na albarkatun man fetur, bayan da Obasanjo ya zama shugaban kasa biyo bayan da aka yi wa magajin Gowon, Murtala Muhammad kisan gilla a shekarar 1976.

Buhari ya zama Sakataren soji a majalisar koli ta sojojin Nijeriya a shekarar 1977 wacce ita ce kujerar gwamnati a wancan zamanin.

A shekarar 2003 ne Buhari bai samu nasara a kan kujerar shugaban kasa ba, inda Olusegun Obasanjo na jam’iyyar PDP ya kayar da shi.

Buhari dai a shekarar 2007 bai kuma gajiya ba ya sake fitowa inda nan ma dai dan takarar jam’iyyar PDP, Umaru Musa Yar’Adua ya sake hawa kujerar shugaban kasa, wanda duk duniya kowa ya shaidi magudi da rashin sahihancin wannan zaben, amma duk da hakan Buhari bai hakura ba domin kishinsa ga ci gaban kasar nan.

Har-ila-yau, a shekarar 2011 Buhari ya sake tsayawa takarar shugaban kasa, inda nan ma dai Goodluck Jonathan ya dale kan kujerar shugaban kasar.

A shekarar 2014, jam’iyyar APC ta tsaida Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa na zaben 2015 da aka gudanar. Inda a nan hakarsa ta kai ga cimma ruwar zama zababben shugaban kasar Nijeriya. Wakazalika, a shekarar 2019, Buhari ya sake samun tagomashin zarcewa a kan kujerar shugaban kasa bayan zaben da aka fafata.

Buhari ya auri Aisha Halilu tun a shekarar 1989. Suna tare tun daga wancan lokacin, kama-kama har suka haifi ‘ya’ya biyar da jika guda. Haka kuma, yana da ‘ya’ya biyar da matarsa ta farko Safinatu Yusuf ta haifa masa.

Allah ya kara mana masu kishin Nijeriya, barka da zagayowar watar haihuwarka shugaban kasa Buhari; Naku Hassan Hassan, Ku rubuta min tedt akan: 08092621319 ko email: abuna2406@gmail.com. Nagode.

Exit mobile version