Buhari Ba Ya Katsalandan A Gudanarwar NNPC – Kyari

Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC), Mallam Mele Kyari, ya yaba wa Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, wajen bai wa kamfanin wuka da nama wajen gudanar da harkokinsa da kansa ba tare da tsoma baki ba.

Ya bayyana cewa, Shugaban Kasar bai taba yin katsalandan a cikin harkokin gudanarwar kamfanin NNPC ba.

Kyari ya bayyan haka ne a Jihar Sakkwato lokacin da yake gabatar da jawabi a jami’ar Usmanu Dan Fodiyo wajen lakcan farkon shekarar 2021.

Ya bayyana cewa, shugabannin gudanarwa na kamfanin NNPC, sun sami damar gudanar da harkokin NNPC ba tare da saka bakin shugaban kasa ba.

“Wanna abun alfahari ne, domin wannan hanya ce da za ta bamu damar gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyanmu musamman ma na rarraba gas a ko’ina a fadin kasar nan,” in ji Kyari.

Shugaban kamfanin NNPC ya bukaci gwamnoni da cibiyoyi  da ke nahiyar Afirka a kan su sumar da kimiyya da karkira wannan zai sa a samu damar magance karancin makamashi da na tattalin arziki wanda ke shafar mutanen yankin.

Ya jaddada cewa, akwai bukatar gwamnatocin Afirka da sauran cibiyoyi da su samar da kimiyya da karkira wanda zai sa a sami isasshen makamashi, domin samar da kamfanoni masu yawa da ayyukan yi da kuma ci gaban tattalin arziki. Kakakin kamfanin NNPC, Dakta Kennie Obateru shi ya bayyana hakan a jiya lokacin da yake zantawa da manema labarai a jiya.

Ya bayyana cewa, NNPC a matsayinta na babban kamfanin mai a yankin Afirka ta gina sabon ginin kimiyya da kirkira na harkokin kasuwanci wanda ake tsammanin zai taka mahimmiyar yawa a bangaren makamashi a nan gaba kadan.

“NNPC ta shirya mahimman kayan aiki wanda zai kawo harkokin kasuwancin makamashi a yankunan Afirka. Mun dauki  wannan mataki ne a matsayinmu na babban kamfanin mai a yankin Afirka wanda zai ba su damar samun nasara a bangaren makamashi,” in ji shi.

Shugaban kamfanin NNPC ya yi maraba da dangantaka shi da wannan jami’a da kuma kwararrun kamfanoni wadanda suke gudanar da cikken bincike domin samun nasara a kan bangaren makamashi.

A cewarsa, samar da makamashi  ba zai kankama ba  har sai an samu nasarar juba jari a wannan bangare, wajen samar da kudade da kulawa da bangaren da kakarin masu ruwa da tsaki da bayar da gudummuwa a bangaren abban more rayuwa da samun muhallin gudanar da kasuwanci wanda zai kawo sauyi. Ya kara da cewa, bangaren makamashi yana kawo hanyoyin bunkasa rayuwar mutane musamman ma a kasashe masu tasowa.

Da yake gabatar da jawabi a wajen taron, babban bako kuma gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa, kamfanin NNPC karkashin shugabancin Kyari ya sake samun dai-daituwa lamura musamman ma a bangaren mai da gas, wanda ake dakon majalisar kasa ta amince da dokar mai domin inganta fannin yadda ya kamata. Haka kuma,Tambuwal ya yi kira ga majalisar kasa da ta tabbatar da cewa, ta amince da wannan mahimmin doka.

Ya ce, ya kamata ‘yan majalisa su duba kokarin Kyari da kuma sauran shawagannin kamfanin wajen kara musu gwarin gwiwa na amincewa da wannan doka.

Tun da farko dai a cikin jawabin shugaban taron kuma gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewa, kamfanin NNPC a karkashi shugabancin Kyari ya samu nasarar gudanar da kyakkyawan tsari tare da samun nasarar cimma yarjejeniya a tsakanin jami’a da kuma masu ruwa da tsaki.

A nasa bangaren, shugaban jami’ar Usman Dan Fodiyo, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ya mika godiyarsa ga shugaban kamfanin NNPC wajen girmama wannan gayyata da jami’ar ta yi masa. Ya bayyana cewa, an samu nasarar kulla yarjejeniya a tsakanin jami’ar da kuma kamfanin NNPC wajen bunkasa kasuwancin harkokin mai a Sakkwato.

Exit mobile version