Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Nijeriya a matsayin kasa mai zaman lafiya kamar Gambiya, Koriya ta kudu, Slobak, Australia, Bagladesh da Guinea Bissau.
Da yake magana a ranar Alhamis a fadarsa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja yayin karbar wasikun amincewa daga wakilan kasashen shida, shugaban ya bayyana zaman lafiya a matsayin wani abu na gama gari a tsakanin kasashen bakwai baya ga dangantakar ‘yan uwantaka tsakanin Nijeriya da kasashen.
Ya ce, “Baya ga dangantakar ‘yan uwantaka da ke tsakaninmu, abu daya da Nijeriya ta hada kai da kasashenku shi ne zaman lafiya. Zaman lafiya ba a sayan shi, abin so kuma mai muhimmanci ga ci gaba mai dorewa da cimma burin da majalisar dinkin duniya ta sa gaba. Don haka ya zama wajibi a gare mu mu yi aiki tare da kuma bangarorin biyu don samun zaman lafiya mai dorewa. Samun zaman lafiya a duniya yana da muhimmanci don samun wadatar abinci. Kamata ya yi a samar da zaman lafiya da wadatar abinci a lokaci guda.”
Ya tabbatar wa da sabbin jakadun cewa, Nijeriya na da kyakkyawar alakar kasashe da kowace kasar su, kuma akwai bukatar a kara dankon zumunci domin amfanin ‘yan kasa.
Shugaban ya yi amfani da wannan dandalin wajen yin kira ga kasashen duniya da su kara hada kai wajen magance wasu manyan matsaloli a duniya, wadanda suka hada da ta’addanci, tayar da kayar baya, kaurar jama’a, da sauyin yanayi, yana mai sake cewa matsalolin ke ci gaba da haifar da babbar barazana ga rayuwar dan Adam.
Don haka, ya bukaci jami’an diflomasiyya da su himmatu wajen kulla alaka mai karfi, tare da mai da hankali kan samar da hanyoyin hadin gwiwa don tunkarar kalubalen bil-adama da na yanayi.
Ya ce, “Ina so in dora muhimmanci a kan bukatar mu hadu don magancewa tare da shawo kan kalubalen da muke fuskanta na ta’addanci, tayar da kayar baya, kaurar jama’a, canjin yanayi, karuwar jama’a, safarar mutane, rashawa, talauci, da yaduwar kananan makamai, wanda dukkansu ko dai musababban rikici ne ko kuma sakamakon hakan.”
“Wadannan kalubalen duk da cewa ta fuskoki daban-daban, suna barazana ga wanzuwar dan adam da dangantakar dan adam. Wadannan kalubalen sun nuna bukatar da ke akwai ga kasashen duniya su hada kai don gano matakan da suka dace don shawo kan wadannan kalubale a duniya,” inji Buhari.
Shugaba Buhari ya fadawa wakilan cewa wannan sabon cutar ta kwayar cutar korona har yanzu ta kasance babbar barazanar dan adam, kasancewar hakan ba kawai ya shafi lafiyar jama’a ba ne, amma har ma yana da mummunar illa ga tattalin arzikin mutane da rayuwar su.
Ya ci gaba da cewa, duk da cewa kasashen duniya sun fara aikin riga-kafi kan cutar, rage yaduwar kwayar da tasirin kamuwa da ita, har yanzu abin damuwa ne.
Yayin da yake maraba da wakilan zuwa Nijeriya yayin da suke daukar nauyin diflomasiyya a hukumance, shugaban ya bukace su da su dora kan nasarorin da magabata suka samu, ya kara da cewa, “Wannan tsohuwar al’ada da kuma aikin da aka sanya a cikin Yarjejeniyar bienna kan dangantakar diflomasiyya ita ce farkon fara aikin ayyukanku a matsayin manyan wakilan kasashenku.”
Shugaban ya karbi wasikun nuna amincewarsa daga Babban Kwamishinan Gambiya, Mista Mohamadou Musa Njie, jakadan Koriya ta kudu, Mista Kim Young-Chae, Jakadan Slobak, Mista Tomas Felid, Babban kwamishinan Ostiraliya, Mista John Gerard Donnelly, Babban Kwamishinan Bangladesh, Mista Md. Masudur Rahman, da Jakadan Guinea Bissau, Dakta Jaao Ribeiro Butiam Co.
Da yake magana a madadin jami’an diflomasiyyar, Babban Kwamishinan na Gambiya ya gode wa Shugaba Buhari kan kyakkyawar tarbar da suka karbe su tun shigowarsu kasar.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen sanya bakin kokarinmu don inganta dangantaka tsakanin kasashenmu ba,” in ji shi.