Gwamnonin Nijeriya 36 sun shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewar gazawarsa wajen samar da tsaro da kuma kasa cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Nijeriya ne dalilan da suka jefa jama’ar kasar nan cikin halin kunci rayuwa da talauci.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnonin, Abdurazaque Bello-Barkindo, ya rabawa manema labarai, ta ce abin takaici ne yaddda gwamnatin tarayya ke neman dora wa gwamnonin laifi dangane da irin talauci da halin kuncin da mazauna yankunan karkarar kasar nan ke fama da su.
- Sinawa Na Jimamin Rasuwar Jiang Zemin
- Alkalai 15 Za Su Gurfana Gaban NJC Kan Zargin Aikata Rashin Da’a
Gwamnonin sun ce a 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin cewar zai fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talaucin da ya addabi jama’a, amma a yau alkaluma sun nuna cewar ‘yan Nijeriya sama da miliyan 130 ne ke fama da talauci, inda suke rayuwa kasa da Dala guda a kowace rana.
Sanarwar ta ce a karkashin gwamnatin Buhari, an kwashe watanni kamfanin man NNPC ba ya iya zuba ribar da yake samu a asusun gwamnati, abin da ya tilasta wa gwamnonin neman mafita ta wasu hanyoyi wajen samun kudaden shiga domin cike gibin kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya domin sauke nauyin da ke kansu a bangare noma da raya karkara da ayyukan jinkai da kuma kula da lafiyar jama’a.
Gwamnonin sun kuma caccaki ministan kasafin kudi, Clement Agba, wanda ya zargi gwamnonin da jefa mutane sama da kashi 72 a yankunan karkara cikin talauci da shara karya wajen kauda kan jama’a daga assalin abin da yake faruwa.
Sanarwar ta ce abin sani shi ne, aikin farko da ya rataya a kan gwamnatin tarayya, shi ne kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a wajen samar da tsaro, domin aiwatar da harkokin ci gaba, amma abin takaici gwamnatin tarayya ta gaza a wannan bangaren, inda ta bar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane suka mayar da kasar dandalin kashe jama’a da sace mutane a gidajensu da makarantu da kasuwanni da kuma gonaki.
Gwamnonin sun ce tabbas gazawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ke jagorancin gwamnatin tarayya, ne ya haifar da dalilan kasa noma da samar da abinci da kuma harkokin kasuwaci a yankunan karkara, saboda yadda zaman lafiya ya gagara, abin da ya hana mutane zuwa gonakinsu da kuma kasuwanni.
Wannan martini na zuwa ne ya biyo bayan zargin da ministan kasafin kudi, Clement Agba, ya yi wa gwamnonin, inda ce sun mayar da hankali wajen gina gadodin sama da filayen jiragen sama, maimakon bunkasa rayuwar jama’ar karkara.