Buhari Ya Ba Guinea Bissau Tallafin Dala 500,000

A matsayin Shugaban Kasa Buhari na shugaban hukumar ECOWAS, ya aika da ministan harkokin wajen Nijeriya, Mista Geoffrey Onyeama a matsayin wakilinshi na musamman zuwa kasar Guinea Bissau.

A sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya fitar yau Juma’a a Abuja, ya Bayyana cewa ministan zai kai ziyarar aiki zuwa Guinea Bissau tare da rakiyar babban jami’in ECOWAS, Mista Jean-Claude Brou.

Garba Shehu ya shaida cewa wannan ya biyo bayan bukatar taimako da kasar ta Guinea Bissau ta yi ne, inda Shugaban Kasa Buhari ya amince da ya tallafa musu.

Tallafin da Shugaba Buhari ya mu su sun hada da na’urar zabe guda 350, babur 10, mota kirar Hilux guda biyar da kuma makudan kudi har dalar Amurka 500,000.

Buharin ya ce yana fatan za a gudanar da zaben kasar cikin nasara, sannan zaben zai taimaka wajen samar da zaman lafiya mai daurewa a kasar.

Har wa yau Ministan zai kai ziyara birnin Kwatano, na kasar Benin, don isar ga sakon Shugaban Kasa Buhari ga Shugaba Patrice Talon na Benin din.

Exit mobile version