Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, ya kuma bukaci a gaggauta kama maharan da suka kai hari Zangon Kataf a Jihar Kaduna tare da hukunta su.
“Akwai harin da aka kai wa ‘yan kasa da ba su ji ba su gani ba a jihar, kuma dole ne jami’an tsaro su dauki matakin da ya dace don kawo karshen hakan,” in ji shugaban kasar a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar.
- Gwamnatin Osun Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Hutu Saboda Zabe
- ‘Yansanda Sun Cafke Mataimakin Shugaban APC Na Jihar Edo
Ya kara da cewa “Ina mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda aka kashe a wadannan munanan hare-haren.”
Zangon Kataf na Kudancin Kaduna, kuma yana fama da hare-haren ‘yan bindiga na tsawon lokaci.
Hare-haren ya sanya dubban mutane tserewa daga yankin.
Da dama kuma sun rasa rayukansu, yayin da wasu marasa adadi suka jikkata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp